Hukumar Shirya Jarabawar Yammacin Afrika (WAEC) ta soke rajistar makarantun sakandire 61 a Jihar Kogi bisa samunsu da laifin tafka satar amsa a jarabawar WAEC ta shekarar 2022.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar, Mista Wemi Jones, ne ya bayyana hakan a garin Kabba a ranar Alhamis, yayin da ake gudanar da rabon karshe na raba littafan Physics ga manyan makarantun sakandire 95 da ke gundumar Kogi ta Yamma a karkashin shirin daukar dalibai da horar da ma’aikatar.
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi
- Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsummar Jego
A cewarsa, WAEC ta gabatar da irin wannan korafin a shekarar 2019 inda makarantun sakandire 51 a jihar suka shiga hannu kan lamarkn.
Ya kara da cewa al’amura sun fara daidaita a shekarar 2020, 2021 inda aka rage yawan makarantun da WAEC ta soke rajista daga 51 zuwa daya sakamakon gargadin da ma’aikatar ilimi ta yi wa shugabannin makarantun.
Kwamishinan ya koka da cewa a ranar Alhamis din makon nan ne jami’an hukumar WAEC suka aike da wasika zuwa ofishinsa da ke nuna cewa makarantun sakandire 61 a jihar na da wajen aikata satar amsa a jarabawar 2022.
“Ma’aikatar ilimi za ta kafa wani kwamiti da zai binciki wannan abin kunya kafin mu sanya takunkumin da ya dace don ya zama izina ga wasu.
“Muna sane da cewa lokacin da WAEC ta karbi kudin rajistar Naira 23,000, shugabannin makarantu sun karbi sama da N40,000 a wajen dalibai.”
Kwamishinan, wanda kuma ya koka kan yadda ake samun wasu manyan makarantu masu zaman kansu a jihar ba bisa ka’ida ba, ya bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba ma’aikatar za ta murkushe su.