Hukumar bincike da bunkasa kaya ta kasa (RMRDC) ta bayyana cewa, ana yin girbin Aya ne sau biyu a kowace shekara.
A cewar Hukumar, ana kuma shuka Ayar ne a watan Afirulu, inda ake girbe ta kuma a watan Nuwamba.
Hukumar ta kara da cewa, noman Aya domin kasuwanci a duk shekara na samar wa da Nijeriya kimanin Naira miliyan 20.
Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, Aya na taimaka wa kiwon lafiyar Dan’adam, sannan kuma tana dauke da sinadarin bitamin E da C, wadanda ke taimakawa wajen kare bil Adama daga kamuwa da cututtuka.
- PDP Ta Lashe Zaɓen Shugabanin Ƙananan Hukumomin Bauchi Gaba Ɗaya
- EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
Kazalika, tana kara samar da hanyoyin kudin shiga, musamman a wannan yanayi na matsin tatattalin arziki, a wannan kasa Nijeriya, akwai kuma matukar muhimmanci mutum ya samar wa kansa wasu hanyoyin na kudin shiga.
A bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa; hanya ce ga wanda ya zuba jarinsa a fannin, zai iya kara samar wa da kansa kudaden shiga.
Sai dai, akasari an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya, musamman ma kuma a Jihar Katsina.
Haka zalika, fannin na samar da ayyukan yi kodai na kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba.
Bugu da kari, Aya na taimawa wajen inganta lafiyar jikin Dan’adam, kara karfafa kashin jikin mutum, daidaita sigan da ke jikin bil Adama da dai sauran makamantansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp