Ma’aikatar Hajj ta ƙasar Saudiyya ta yi gargaɗi kan akwai yiwuwar yau Litinin, za a tsananin zafi da kai iya kaiwa maki 49 na ma’unin Celsius, inda ta ja shawarci maniyyata da su tabbatar su na yawo da lema domin gujewa rana, tare da shan ruwa sosai akai-akai.
Wannan na zuwa ne bayan mutane da dama sun rasu sakamakon tsananin zafi a ‘yan kwanakin nan, daidai lokacin da maniyyata ke shirin kammala aikin Hajjin bana a Makkah.
- Yadda Jami’an Saudiya Da Nijeriya Suka Yi Rangadin Wuraren Aikin Hajji
- Hajjin Bana: Yau Litinin Ita Ce Ranar Ƙarshe Ta Jigilar Maniyyata Zuwa Ƙasar Saudiyya
An yi hasashen cewa a yau ranar Litinin, tsananin zafi a birnin Makkah zai iya kaiwa maki 49 a ma’unin Celsius, a daidai lokacin da mahajattan ke ci gaba da jifar shaiɗan a Mina.
Rahoton ma’aikatar lafiya ta ƙasar Saudiyya ya nuna ko a jiya Lahadi, kaɗai an samu sama da mutum 2,700 da zafi ya yi wa illa.