Kasashen Larabawa na yankin Gulf sun nemi kamfanin Netflix ya cire dukkan fina-finan da suka sabawa dokokin Musulunci da al’adun tarbiyya, kamar yadda kafar yada labarai ta Saudiyya ta ruwaito.
A wata sanarwa da kungiyar kasashen yankin Gulf ta fitar ta yi gargadi cewar wasu fina-finai na baya-bayan nan da aka yi don yara sun saba wa dokokin musulunci.
- Lauyoyi Sun Maka Ado Gwanja, Safara’u, 442 Da Wasu ‘Yan TikTok A Kotu
- Buhari Ya Kaddamar Da Wani Kwamiti Da Zai Sake Duba Bukatun Kungiyar ASUU
Kafar talabijin ta Saudiyya ta nuna wasu bidiyo da aka dusaseh fuskarsu na katun din fim din Jurassic World: Camp Cretaceous, wanda aka nuna wasu yara mata biyu suka nuna suna son juna tare da sumbatar juna.
Gidan talabijin na Al Ekhbariya da ya nuna wani sashe na fim din da wani kamfanin Faransa na Cuties ya shirya, ya sanya take kamar haka “bidiyon da ke nuna rashin da’a da rusa tarbiyya wanda ke barazanar lalata tarbiyyar yara.”
A wani bidiyon da Al Ekhbariya ta wallafa a shafinta na Intanet, ta yi zargin cewa fim din na “yada luwadi da madigo ne.”
Hakazalika gidan talabijin din ya yi hira da mutane da dama da suka yi irin wanan zargin tare da kiran hukumomi su dauki mataki cikin gaggawa.
An tuntubi Netflix da ya cire bidiyon, da kuma duk wasu fina-finai da aka shirya don yara, tare da tabbatar da bin dokoki,” kamar yadda sanarwar hadin gwiwa daga hukumar kula da fina-finai ta Saudiyya da ta kula da kafafen yada labarai.
Hukumomi za su sa ido don ganin ko an bi umarnin, tare da daukar matakan shari’a idan har aka ci gaba da yada fina-finan”, kamar yadda suka yi gargadin.
Babu wani martani daga kamfanin Netflix, duk da cewa Saudiyya ba ta da wasu dokoki na damar zabar jinsi, amma yin luwadi da madigo da zina haramun ne a kasar.
A karkashin dokokin Musulunci na kasar dai, hukuncin duk wanda aka kama da laifin luwadi ko madigo hukuncin kisa ne ko bulala, ya dangata girman laifin.