Mahukuntan Kasar Saudiyya sun kama wani mutum wanda ya yi tattaki daga Kasar Yemen don yi wa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, aikin Umrah da nufin samun rahamar ubangiji.
Mutumin dan Kasar Yemen da ba a bayyana sunansa ba, ya wallafa wani gajeran bidiyo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna shi a gaban dakin Ka’abah yana addu’o’in neman rahama ga Sarauniyar wadda ta mutu ranar 9 ga watan Satumba, 2022 ta na da shekaru 96.
- Dogara, Babachir Sun Gana Da Shugabannin Kiristoci Don Daukar Matsaya Kan Zaben 2023
- Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab Sama Da 100
Bidiyon ya nuna mutumin rike da wani allo mai dauke da rubutun ‘ibadar aikin Umrah ga Sarauniya Elizabeth, da fatan Allah ya karbe ta a cikin salihan bayi’, bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.
Tuni dai wannan bidiyo ya haddasa cece-kuce yayin da mutane suka rika kiraye-kirayen ganin lallai mahukuntan kasar sun kame mutumin tare da hukunta shi.
Bisa dokokin Saudiyya dai, babban laifi ne gudanar da aikin hajji ko Umrah rike da wani allon bayanai kan wani mutum ko kuma furta wasu kalamai da ba kalmar Allah ba.
Haka zalika, duk da cewa addinin Islama ya halatta yi wa matattu aikin Hajji ko Umrah, amma hakan baya halatta ga wanda ba musulmi ba.
Jami’an tsaron Harami sun kame mutumin wanda suka ce zai fuskanci hukunci dai-dai da laifinsa, sai dai basu bayar da bayani kan shekarunsa da kuma dalilinsa na aikata hakan ba.