Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari, idan aka yi la’akari da dan abin da take samu wurin tafiyar da al’amuran kasar nan.
Buhari, ya yi kalaman ne yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin Jihar Imo da ke birnin Owerri a ranar Talata, bayan bude wasu manyan ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma ya yi.
- Saudiyya Ta Kama Mutumin Da Ya Yi Umrah Saboda Sarauniyar Ingila
- Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Mulkin Soji A Sudan
Shugaba Buhari, ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin gudanar da ayyuka da dama duk da kudaden da take samu ba su taka kara sun karya ba.
”Wannan gwamnati ta yi namijin kokari sosai. Dole na fada saboda wadanda alhakin fadar hakan ya rataya a wuyansu ba sa yin haka. Ban san me ya sa ba,” in ji Shugaba Buhari.
Ya kuma jinjina wa gwamnatinsa bisa nasarar da ta samu na gurgunta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a Kudu maso Gabas, a rikicin da ya ce ya gada daga gwamnatin PDP a 2015.
Shugaban ya kuma yi jinjina ga gwamnan jihar ta Imo kan gayyatar shi a karo na biyu cikin shekara daya don ya bude ayyukan da ya aiwatar.