Kawo yanzu Saudiyya wadda ita kadai ce ke neman daukar bakuncin Kofin Duniya na 2034, ta gabatar da bukatar neman daukar gasar a hukumance kuma a watan Oktoba kasar da yankin Gulf ta nuna muradin daukar gasar a zahiri, bayan Australia ta janye daga neman bakuncin gabanin cikar wa’adin da FIFA ta sanya.
FIFA ce za ta tabbaatar da amincewa kan wannan bukata a wannan shekarar, sannan shugaban hukumar kwallon kafa ta Saudiyya Yasser Al Misehal ya ce, za a amince da bukatar ta Saudiyya saboda yadda take samun ci gaba cikin gaggawa.
- An Dakatar Da Bellingham Daga Buga Wasanni Biyu Na Laliga Sakamakon Rikici Da Alkalin Wasa
- An Buga Jadawalin Zagaye Na 16 Na Gasar Europa Da UEFA Conference League
Al Misehal ya kara da cewa yana da muhimmanci su gaya wa daniya labarinsu domin sun samu wani irin ci gaba mai girma daga bangaren wasan mata da na maza, bukatar ta su wata takardar gayyata ce ga duniya ta zo ta ga yadda tafiyarsu ke cike da albarka.
Duk da cewa ita kadai ce ta nemi daukar nauyin gasar, dokokin FIFA na bukatar sai an shigar da bukatar neman hakan a hukumance kuma amma Saudiyya ta zuba jari da ya kai fan biliyan biyar a bangaren wasanni tun 2021. Kazalika Yarima ya bayyana cewa wannan na daya daga cikin hanyoyin fadada hanyoyin samun kudin kasar.
Gasar za ta zama ita ce ta farko da kasashe 48 za su halarta a kasa guda daya saboda kasashen Moroko da Portugal da Sifaniya su ne za su dauki nauyin gasar ta 2030 a wani mataki na hadin gwiwa, yayin da za a fara wasanni ukun farko za a yi su a Uruguay da Argentina da Paraguay.
Gasar 2026 da za a yi, za ta zama ta farko da kasashe 48, amma za a gudanar da ita ne a kasashen Amurka da Medico da kuma Canada, sanan karbar bakuncin gasar Kofin Duniya a Saudiyya, abu ne da aka jima ana burinsa, duba da yadda kasar ke zuba jari a fagen wasanni a shekarun baya-bayan nan.
To amma duk mutumin da ke la’akari kan yadda kasar ta gudanar da gagarumin sauye-sauye – a fannin wasannin kwallon golf ta hanyar shirya gasar wasan, ko yadda kasar ta mamaye karbar bakuncin manyan gasar damben zamani, ko kuma yadda kasar ta zuba jari a fagen kasuwancin ‘yan wasan kwallon kafa – hakan ba zai zama abin mamaki ba.
Yawan ganawa da shugaban FIFA, Gianni Infantino ke yi da Yariman Saudiyya a shekarun baya-bayan nan, ka iya zama wata alama ta yadda kasar ke kara zama mai karfin fada-a-ji a fagen wasanni.
To amma, duk da matsayin kasar a fagen wasanni, batun daukar nauyin gasar Kofin Dunya a Saudiyya zai bai wa mutane da dama mamaki domin a yanzu da kasar ke da kusan tabbacin damar daukar nauyin gasar nan da shekara 11 masu zuwa, kasar za ta iya fuskantar ce-ce-ku-ce fiye da yadda Katar ta fuskanta a shekarar da ta gabata.
Kama daga matsalolin da suka shafi tauye hakkin bil-adama, da yadda FIFA ke tafiyar da batun takarar daukar nauyin gasar, ga kuma batun sauya lokacin gasar, da kuma walwalar ‘yan wasa sakamakon yiwuwar gudanar da gasar a lokacin hunturu, saboda matsancin zafi da ake fuskanta a lokacin bazara a kasar.
Ganin yadda aka fadada kasashen da za su halarci gasar zuwa 48, yawan sauye-sauyen da kasar za ta yi sun zarta na Katar, sakamakon gina muhimman wuraren da ake bukata, na kara saka shakku game da yadda kasar za ta tunkari wanna gagarumin sauyi.
Masu suka da dama na kallon hakan a matsayin nuna sha’awa a ‘fagen wasanni’ ga kasar da ke zama babbar mai fitar da man fetur a duniya kuma daya daga cikin kasashen da suke kashe kudi a bangaren wasannin kwallon kafa.
Haka kuma akwai fargabar tauye hakkin mata, da haramta neman jinsi, da takaita ‘yancin fadar albarkacin baki, da ci gaba da yanke hukuncin kisa, ga batun zargin kisan fitaccen dan jaridar nan Jamal Khashoggi a 2018, tare da zargin hannun kasar a yakin Yemen.
To sai dai hukumomin Saudiyya sun sha musanta haka, suna masu cewa bukatarsu ta daukar nauyin gasar, zai taimaka wajen zamanantar da kasar, wajen inganta harkokin wasanni, tare da karfafa wa matasa gwiwa, bunkasa yawon bude-ido, da bunkansa hanyar samun kudin shiga ga kasar, kafin karewar man fetur, tare kuma da hada kan kasashen duniya.
Kasar ta nuna irin ci gaban da ta samu a fagen kwallon kafar mata alal misali, suna masu cewa wannan wata dama ce ta bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa, bayan samun nasarar daukar nauyin wasu gasanni.
Da karfafa gasar kwallon kafar kasar ta ‘Saudi Pro League’ da sayen kungiyar Newcastle United, da kuma shirin kasar na daukar nauyin gasar Kofin Duniya ta kungiyoyi a lokacin hunturu, ga kuma daukar nauyin gasar kasashen Asiya ta AFC a shekarar 2027.
To sai dai yayin da aka fi samun sha’awar kwallon kafa a Saudiyya fiye da Katar, mutanen da ke halartar kallon gasar Pro League sun ragu a wanna kaka saboda wasu dalilai.
To amma ko ma mene ne manufar jagororin kasar, kasancewarta kasa daya tilo da ke takarar karbar bakuncin gasar a 2034, zai rage wa FIFA wahalar yanke hukuncin wanda za ta ba wa.
Sanarwar FIFA na gabatar da bukatar karbar bakuncin gasar ta 2034 a farkon wannan wata ya zo wa mutane da ba-zata, kasancewar FIFA ta kayyade cewa dole kasar da za ta yi takarar ta fito daga yankin Asiya ko Oceania, tare da bayar da wa’adin kwana 26 ga masu takarar don su bayyana sha’awarsu.
Sai dai bayan sanarwar FIFA, cikin ‘yan mintuna – Saudiyya ta bayyana sha’awarta a hukumance, inda kuma hukumar kwallon kafar yankin Asiya ta nuna goyon bayanta kan matakin na Saudiyya.
Shin alfarma aka yiwa saudiyya?
A wani mataki kuma da wasu ke gani kamar alfarma aka yi wa Saudiyya, FIFA ta sasauta dokarta kan gina sabin filayen wasa, inda a yanzu ake bukatar masu neman daukar nauyin gasar su kasance suna da ginannu filayen wasa hudu (a maimakon dokar yanzu ta filaye bakwai).
A yanzu da Australiya ta dauki matakin janyewa daga takarar, ana ganin ta yi hakan ne don ta san ba za ta iya ja da Saudiyya ba a wannan takara ba musamman wajen gina sabbin filaye.
A watan Maris ne kungiyar shirya gasar kwallon kafa da duniya – wadda ke wakiltar gasar lig na kasashe a duniya – ta bayyana damuwarta kan ikirarin da ta yi na cewa FIFA ba ta tuntube ta ba kan sauya lokacin wasan kwallon kafa a duniya ciki har da kara yawan kasashen da za su halarci gasar Kofin Duniya ta 2026.
Kungiyoyin kare hakkin Bil’Adama sun yi alla-wadai da FIFA
Haka kuma kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta zargi FIFA da yin watsi da dokokinta, tana mai cewa abin kunya ne ga FIFA idan har ta bai wa Saudiyya damar daukar nauyin gasar Kofin Duniya ta 2034, kasancewarta mai tarihin tauye hakkin bil-adama da rashin bayar da dama ga kungiyoyin kare hakkin da’adam don gudanar da ayyukansu, kuma tabbas
hakan na saka shakku kan kudurin FIFA ta tabbatar da ‘yancin dan’adam.
To sai dai FIFA ta ki cewa komai kan batun, to amma ta dage cewa ‘yancin dan’Adam na daga cikin manyan ka’idoji neman daukar nauyin bakuncin gasar kuma Saudiyya za ta kasance daya daga cikin kasashen da daukar nauyin babbar gasar duniya ke janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan.
Alakar neman jinsi haramun ne a Morocco, wadda ke daya daga cikin kasashen da za su karbi bakuncin gasar 2030, kamar yadda yake a Katar, haka kuma batun yake a Saudiyya. Masu goyon bayan auren jinsi, wadanda suka ce ba sa jin za su samu kariya a gasar Kofin Duniyar da ya gabata, a yanzu za su ji ba lallai su halarci gasar biyu masu zuwa ba.
Shin karfin katar da saudiyya ya kawo?
A baya in aka ce karamar kasa irin Katar da makobciyarta Saudiyya za su iya daukar nauyin bakuncin gasar kofin duniya har guda biyu cikin shekara 12, mutane da dama za su yi mamakin hakan. To amma idan aka yi la’akari da dimbin arzikin da kasashen ke da shi da yadda salon FIFA ya sauya musamman karkashin jagorancin shugabanta Gianni Infantino, hakan ba abin mamaki ba ne.
A yanzu ‘yan kasar Saudiyya, za su ci gaba da kare kansu kan abin da suke gani a matsayin munafurci, suna nuni da huldar kasuwanci da mafi yawan kasashen Yamma ke jin dadin kullawa da su.
Suna masu cewa kasashen na jahiltar Saudiyya, kamar yadda tauraron damben boding, Tyson Fury ya fada a baya-bayan nan, bayan ya yi wasa a Birnin Riyadh, inda ya ce bai kamata mutane su yanke wa kasar hukunci kafin su ziyarce ta ba. Hukumomin kasar za su kwatanta da Katar, wadda duk kuwa da sukar da ta sha, ta samu damar daukar nauyin gasar da mutane da dama suka kalla a matsayin nasara.
Amma dai ko ma dai mene ne a yanzu FIFA da Hukumomin Saudiyya na da shekara 11 domin su nuna wa masu shakku cewa za su iya shirya gasar kuma za a iya yin nasara idan an yi abin da ya dace.