Wasu rahotanni daga kasar Saudiyya suna bayyana cewa ba za a bari a sha barasa ba a lokacin gasar cin kofin duniya da kasar za ta dauki nauyi a shekarar 2034. A hirar da aka yi da shi a LBC, jakadan Saudiyya a Burtaniya, Yarima Khalid bin Bandar Al Saud ya ce ba za su bari a sha barasa ba a lokacin buga babbar gasar kwallon kafa ta duniya, har da otal da sauran wurare.
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bai wa Saudiyya izinin shirya gasar kofin duniya a 2034, za a gudanar da ita 2026 a Amurka da Canada da Medico. A cewar jakadan, za a iya samun nishadi ba tare da shan barasa ba – ba ta zama wajibi ba dari bisa dari, idan kowa ya koma kasarsa, sai ya ci gaba da ta’ammali da ita, amma yanzu ba za su bari a sha ba a
- Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
- Ballon D’or: An ZaÉ“e Ni Ne Kamar Yadda Aka ZaÉ“e Ka – Martanin Rodri Ga Ronaldo
lokacin gasar.
Batun ko za a sha barasa a Saudiyya ya taso ne, tun kafin shirya gasar kofin duniya a katar a 2022, wata kasar Musulunci, wadda ta sa ido kan sayarwa da shan barasa. An sauya dokar sayar da barasa a katar kwana biyu a fara gasar kofin duniya, yayin da ‘yan kallo suka samu damar saya a wasu wurare har da otal amma kuma a otel din suka dinga sha saboda doka ne shan giya a cikin jama’a.
An haramta auren jinsi a Saudiyya, ba a yadda mutum ya sauya halitta ba, sai dai Yarima Khalid ya ce muna maraba da kowa zuwa Saudiyya. Ana zargin Saudiyya da yin amfani da shirya wasanni a shekarun baya, domin kawar da hankulan mutane kan yadda take karya hakkin dan Adam, Amnesty International ta ce shirya gasar kofin duniya a Saudiyya zai haifar da take hakkin dan’adam dayawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp