A yayin da kwanuka 25 ne suka rage a cike wa’adin da aka baiwa jami’an tsaron kasar nan na kawo karshen ‘yan bindiga da kuma ‘yan ta’adda, a iya cewa, lokaci na kara kure wa jami’an na cika wa’adin ranar 31 ga watan disambar 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba su.
A watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta shelanta cewa, rashin tsaron da Nijeriya ke fuskanta za ta kawo karshen hakan a watan Disambar 2022.
Ministan kula da harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce, Buhari ya kebe watan Disambar a matsayin watan da jami’an tsaron za su maido da dawwamammen zaman lafiya a daukacin fadin kasar.
Ya ce, daga cikin nasarorin da aka samu domin a cimma wamnan wa’adin na shugaban kasa, a ranar 14 ga watan Nuwambar 2022, gwamnatin ta sanar da cewa, tana neman ‘yan ta’adda 19 tare da sanya tutwicin naira miliyan biyar ga duk wadanda ya fallasa inda suke.
A cewar wata majiya ta soji, babu daya daga cikin ‘yan ta’addar 19 da aka iya cafko wa har zuwa yau duk da tukwicin naira miliyan biyar da gwamnatin ta sa.
Sai dai, sakatare janar na cibiyar (IIPS) Dakta Abdullahi Mohammed Jabi, ya danganta wancan tabbacin na kawo karshen ta’addan cin da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin magana ce kawai ta siyasa.
Abdullahi ya ce, koda yake, sojoji sun yi kokari wajen yakar ‘yan ta’adda a kasar, amma ana bukatar da su kara jajirce wa don kawo karshen hakan a kasar.