A yau ne, bankin raya kasashen Asiya, ya fitar da rahotonsa kan hasashen ci gaban Asiya na shekarar 2023, inda a cikinsa ya bayyana cewa, saurin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin zai kara habaka ci gaban shiyyar da ma duniya baki daya. Rahoton ya yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin, zai kai kashi 5 cikin 100 a wannan shekara, ana kuma sa ran karuwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya zai kai kashi 4.8 bisa 100.
Rahoton ya yi imanin cewa, saurin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, zai taimaka ga karuwar kayayyakin da ake fitarwa a yankin Asiya da tekun Pasifik, da habaka cinikayya da yawon shakatawa a yankin, da kara karfafa gwiwar ci gaban tattalin arziki. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp