Gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele a jiya Talata, ya tabbatar da cewa babu wani dan Nijeriya da zai yi asarar kudinsa sakamakon sauya fasalin kudi da gwamnati ta yi. Ya kara da cewa manufar sauya kudin don inganta tattalin arzikin Nijeriya ne baki daya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa ba su rufe kofar sauraron korafe-korafe ba kan yanke ranar da za a daina amfani da tsoffin kudin kasar da aka sauyawa fasali.
Emefiele ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da kwamitin majalisar na wucin gadi wanda ya tattauna da shi da manyan jami’an bankunan kasuwanci a kan wa’adin daina amfani da tsoffin kudin da aka sauyawa fasali.
“Babu dan Nijeriya da zai yi asarar kudinsa,” in ji shi, ya bayyana hakan ne domin neman hadin kan Majalisar Dokokin kasar don tabbatar da nasarar shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp