Jam’iyyun siyasa 13 daga cikin jam’iyyu 18 a Nijeriya sun yi barazanar kaurace wa babban zaɓen ƙasar da ke tafe matukar Babban Bankin Ƙasar ya ƙara wa’adin amfani da tsoffin kuɗi a ƙasar.
BBC ta rawaito cewa, Jam’iyyun sun ce ba za su shiga zaɓen ba matuƙar CBN ya sake tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin.
- Gwamnonin Kaduna, Kogi Da Zamfara Sun Maka Gwamnati A Kotu Kan Karancin Kudi
- PDP Ta Zargi Tinubu Da APC Kan Boye Sabbin Kudi Don Sayen Kuri’u
Gamayyar ƙungiyar shugabannin jam’iyun, waɗanda suka yaba wa shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari, kan sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, sun dage cewa dole a tabbatar da tsarin.
Shugaban Jam’iyyar Action Alliance A.A Kenneth Udeze, wanda ya yi wa manema labarai jawabi, ya ce ”muna bayyana cewa akalla jam’iyyu 13 daga cikin jam’iyyun ƙasar nan 18 ba za mu shiga zaɓen da ke tafe ba matuƙar aka dakatar ko a aka soke ko aka tsawaita wa’adin fara amfani da sabbin takardun kuɗi”.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara suka kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙolin ƙasar, suna neman kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da tsarin wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi.
Matakin da gamayar jam’iyyun suka yi watsi da shi.
A makon da ya gabata ma dai gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka gana da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Inda suka buƙace shi da ya sake tsawaita wa’adin amfani da sabbin takardun kudi, sakamakon wahalhalun ƙarancin kudin da jama’ar ƙasar ke fuskanta.
To sai dai a martanin da ya mayar, shugaban ƙasar ya alƙawarta duba tare da magance matsalar cikin kwanaki bakwai.