Ministan Raya Ma’adanan ƙasa, Dr. Dele Alake, ya bayyana cewa ɓangaren ma’adanan ƙasa na Nijeriya ya samu kuɗin shiga da ya kai Naira biliyan 38 a shekarar 2024, saɓanin Naira biliyan 6 da aka samu a shekarar da ta gabata. Wannan ci gaba ya samu ne duk da cewa an samu kashi 18 cikin 100 ne kawai daga cikin Naira biliyan 29 da aka ware wa ɓangaren a kasafin kuɗi.
Alake ya danganta nasarar da aka samu da sauye-sauyen manufofin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, musamman matakan da suka shafi kara darajar kayayyaki a cikin gida da kuma tsaurara tsarin bayar da lasisi. Ya ƙara da cewa hakan ya jawo zuba hannun jari sama da dala miliyan 800 a fannin sarrafa ma’adanai.
- Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi
- Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno
A wata tattaunawa da aka yi da shi a wani shirin gidan gwamnati da ke tafe domin bikin cikar gwamnatin Tinubu shekaru biyu, Alake ya bayyana yadda sabbin matakan suka ƙarfafa ƙwarin gwuiwar masu zuba jari.
Ya lissafo wasu manyan jarin da suka haɗa da masana’antar sarrafa lithium da ta kai dala miliyan 600 a kan iyakar Kaduna da Neja wadda za a buɗe a wannan shekara, da wata masana’anta ta dala miliyan 200 a gefen Abuja da ake kammalawa, da kuma wasu guda biyu a jihar Nasarawa da ake sa ran kammalawa kafin ƙarshen shekarar 2025.
Alake ya jaddada cewa yanzu gwamnati ba za ta ba da lasisin hakar ma’adanai ba sai an tabbatar da gina masana’antar sarrafawa a gida. “Lokacin fitar da ma’adanai daga rami kai tsaye zuwa ƙasar waje ya wuce. Lokacin da muka fara aiki, gaba ɗaya ɓangaren yana samar da Naira biliyan 6 a shekara, yanzu kuwa Naira biliyan 38 ake samu — kuma har yanzu yana karuwa,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp