Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun cigaba sannu a hankali, inda ya danganta hakan da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar baƙuncin mambobi da sababbin shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) da suka kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa.
- Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon
- An Fara Taron Nishan Karo Na 11 Game Da Wayewar Kai A Duniya
Yayin da ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubale, Ministan ya ce gwamnati na samun cigaba a hankali kuma tana samun nasarar rage tsananin matsalolin da ake fuskanta.
Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci.
“Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin arziki ba tukuna. Gaskiya ne! Ni ma na yarda. Amma ba za mu ce babu cigaba ko kaɗan ba.”
Ya ƙara da cewa: “Ko hukumomin ƙididdiga na duniya suna fara ba Nijeriya kyakykyawan matsayi. Muna ganin alamu na ɗagawa a hanyar da ake tafiyar da tattalin arzikin mu.”
Idris ya ce manyan matakan sauyi kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi suna fara nuna tasiri mai kyau a ƙasar nan.
Haka kuma ya bayyana cewa sama da ɗalibai 300,000 ne suke cin gajiyar shirin bayar da rancen karatu na gwamnati, wanda ke ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da kuma ciyar da su.
Ya ce: “Saboda wannan manufa da aka tsara ta gwamnati, sama da ɗalibai 300,000 na Nijeriya da a da ba za su iya zuwa makaranta ba ko kuma da suka riga suka bar makaranta, yanzu suna da damar komawa makaranta domin gwamnati tana biya masu kuɗin makaranta da na ciyarwa. Ba a taɓa samun irin wannan ba.”
A kan batun tsaro, Ministan ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai masu ƙarfi don shawo kan matsalolin tsaro, inda ya ce dakarun soji na samun nasarori a yaƙi da masu laifi a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya roƙi kafafen yaɗa labarai da su goyi bayan ƙoƙarin da rundunonin tsaro suke yi, tare da guje wa bai wa masu laifi muhimmanci fiye da kima.
“Ina ta faɗa tun da farko cewa ba daidai ba ne mu a matsayin mu na ‘yan jarida mu riƙa ba waɗannan masu laifi, masu tayar da ƙayar baya, ‘yan ta’adda ko ɓarayi ko duk yadda za a kira su, fifiko fiye da ‘yan Nijeriya nagari,” inji shi.
Ya ce ya kamata kafafen watsa labarai su riƙa bayyana nasarorin da sojoji suke samu da sadaukarwar su, maimakon maida hankali kawai a kan hare-hare da rashin nasara.
Idris ya bayyana cewa ko da yake aikin kafafen watsa labarai ne su riƙa sa ido kan gwamnati ta hanyar suka mai amfani, wajibi ne su kuma riƙa bayyana nasarori da cigaban da ake samu.
A martanin sa kan Rahoton Gyaran Dokoki da ƙungiyar ta gabatar, Ministan ya ce zai tattauna da Ministan Shari’a kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, tare da kafa kwamitin musamman a ma’aikatar sa domin nazarin rahoton.
Ya jaddada cewa manufar gwamnatin Tinubu tana daga cikin ginshiƙan dimokiraɗiyya ita ce kare ‘yancin faɗar albarkacin baki da ‘yancin kafafen yaɗa labarai.
Sai dai ya ja hankalin ‘yan jarida da su riƙa amfani da wannan ‘yanci cikin kishi da kishin ƙasa, tare da riƙon gaskiya da haɗin kai don ci gaban ƙasa.
Idris ya taya sababbin shugabannin ƙungiyar murna, tare da bayyana shirin sa na ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da kafafen watsa labarai.
Tun da farko a jawabin sa, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya, Dakta Sebastian Abu, ya bayyana cewa tawagar ta kai ziyara ofishin Ministan ne don gabatar da rahoton Kwamitin Sauya Dokokin Ƙungiyar a hukumance.
Ya bayyana cewa rahoton ya nuna wasu tsofaffin dokoki a kundin tsarin mulki da suka zama ƙalubale ga ‘yancin aikin jarida a Nijeriya, waɗanda ya dace a duba ko a cire su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp