Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta karyata labarin karya a kan tsofaffin takardun kudi na Naira da aka wallafa a sahihin shafinta na Instagram da Facebook a ranar Talata, inda ta nemi jami’an tsaro da su cafko wanda ya yada labaran karyar sannan a hakunta shi.
Uwargidan shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, barawon shafin na ta ya danganta labaran karyar ga CBN, inda yace, an tsawaita cigaba da amfani da tsoffin takardun kudi na N500 da N1000.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa tun da farko CBN ta karyata labaran karyar da aka wallafa a sahihin shafin Instagram da Facebook na uwargidan shugaban kasar.
Labarin karyar da aka yada a kafafen sada zumunta guda biyu na uwargidan shugaban kasar, ya nuna cewa, babban bankin kasa ya amince a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 har zuwa ranar 1 ga watan Mayu, 2023 sabanin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan daina amfani da tsoffin kudin a fadin kasar.
Sai dai Aisha Buhari, wacce ta bayyana a shafinta na Facebook sa’o’i kadan bayan fitar labaran karyar a shafinta a ranar Talata, ta yi fatali da sakon, inda ta ce, ta bayar da umarnin cire bayanan karyar nan take.