Gwamnatin tarayya ta bukaci kotun kolin Nijeriya da ta yi watsi da karar da gwamnatocin jihohi uku suka shigar na kalubalantar kudirinta na ranar daina amfani da tsoffin tsabar kudin Naira a kasar.
A kwanakin baya ne dai gwamnatocin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka garzaya kotun koli, inda suka bukaci ta dakatar da manufofin gwamnatin tarayya kan ranar daina amfani da tsoffin kudin Naira 200 da 500 da 1000.
A cewar jihohi ukun, tsarin ya jefa ‘yan kasa cikin wani hali mawuyaci da basu taba gani ba.
A ranar Laraba ne kotun koli ta bayar da umarnin dakatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu da za a daina amfani da tsoffin takardun kudin inda ta dage shari’ar zuwa ranar 15 ga Fabrairu, 2023.
Amma, Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, SAN, a madadin Gwamnatin Tarayya ya shigar da karar farko na kalubalantar karar, inda ya yi kira ga Kotun Koli da ta yi watsi da karar da gwamnonin suka shigar.
AGF, ta bakin lauyansa, Mista Mahmoud Magaji, SAN, ya bayyana karar a matsayin cin zarafin kotu.