Yayin da fafutukar neman nasara a zaɓen shekarar 2027 ke ɗaukar zafi, bayan ƙaddamar da shugabancin riƙon ƙwarya na shugabancin jam’iyyar ADC a matakin ƙasa, magoya bayan jam’iyyar PDP da wasu jam’iyyun adawa sun fara komawa sabuwar jam’iyyar adawa ta haɗaka a jihar Borno.
Fitattun ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun bayyana ADC a makon da ya gabata a matsayin sabon dandalin haɗin gwuiwa don ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC a babban zaɓen 2027.
- ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
- ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 9, Tare Da Jikkata Wasu Mutum 4 A Borno
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna tsohon ɗan takarar gwamna a PDP kuma jigo a APC, Mattawali Kashim Ibrahim Imam, yana karɓar baƙuncin wasu manyan ƴan siyasa a gidansa da ke Maiduguri, inda aka bayyana cewa sun tattauna batun sauya sheƙa zuwa ADC.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa manyan ƴan adawan Nijeriya guda biyu — Alhaji Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party — sun nuna goyon baya ga sabon dandalin siyasa na ADC. Sai dai gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya musanta raɗe-raɗin cewa shi da wasu gwamnoni guda biyar za su fice daga APC zuwa sabuwar jam’iyyar haɗaka.
Rahotannin sun nuna cewa Idris Mamman Durkwa, tsohon ɗan takarar gwamna, da Hon. Sheriff Banki, wani fitaccen matashi mai samun goyon bayan jama’a, sun jagoranci ficewar dubban mambobi daga PDP zuwa ADC.
Sannan kuma akwai Hon. Mohammed Umara Kumalia, tsohon jagoran ƴan adawa a Majalisar Wakilai; Alhaji Saleh Kida, mataimakin ɗan takarar gwamna na PDP a 2023; da Hon. Abdulrazaq Ahmed Zanna, ɗan takarar majalisa daga Bama, Ngala, da Kala Balge, da dama daga cikin tsofaffin ‘yan takara da shugabannin jam’iyyar da suka fice daga PDP da APC.
A cewar Hon. Banki, wannan babban sauyi da ake gani a jihar Borno na nuna gajiya da gazawar gwamnatin APC a matakin ƙasa da jiha. Ya caccaki shugabancin PDP na jihar ƙarƙashin Hon. Zanna Gadama da cewa sun miƙa wuya ga “matsin lamba daga sama,” wanda hakan ya haifar da ficewar mambobi masu yawa. Ya kuma ce tsadar rayuwa da rashin tsaro sun ƙara jefa mutane cikin ƙunci, wanda hakan ya sa jama’a ke neman mafita daga irin wannan jagoranci.
Ya buƙaci jama’ar jihar su marawa ADC baya, yana mai bayyana ta a matsayin jam’iyyar da za ta dawo da dimokuraɗiyya ta gari tare da ceto al’ummar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp