Wasu rahotanni sun ruwaito cewa, cikin shekaru 4 masu zuwa, Amurka na sa ran sayar wa yankin Taiwan makaman da yawansu zai zarce adadin wa’adin shugaba Donald Trump na farko.
Son kai irin na Amurka a dukkan wasu harkoki da za su amfane ta na kara bayyana, wanda ke kara nuna rashin damuwarta ga yanayin da wasu ka iya shiga, muddin za ta cimma moriyarta.
Kafar yada labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, a wa’adin mulkin Trump na farko, kasarsa ta amince da sayar wa yankin Taiwan makaman da darajarsu ta kai dala biliyan 18.
Za mu iya fahimtar ikirarin Amurka cewa, ba ta goyon bayan ballewar Taiwan domin ba ’yancin kan yankin ta damu da shi ba. Abun da za ta amfana da shi, shi ne sayar wa yankin makamai, tun da moriyarta ta fi muhimmanci maimakon tabbatuwar zaman lafiya da ci gaba.
Ba kadai ga Taiwan ba, duk inda Amurka za ta samu moriya, to ba ta duba mummunan tasirin da hakan zai yi, muddin dai za ta samu abun da take nema. A farkon shekarar nan, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce kayayyakin soja da kasar ta sayar wa kasashen ketare a shekarar 2024, ya kai dala biliyan 318.7 karuwar kaso 29 cikin dari kan na shekarar 2023.
A takaice dai, abun da ake yi shi ne, amfani da tashe-tashen hankali da yake-yake wajen cin riba, inda ake bayyana goyon baya ga masu neman rikici domin ingiza su kashe kudi wajen sayen makamai.
Ya kamata mahukuntan yankin Taiwan su farka daga baccin da suke yi, su gane cewa su kadai suke kidi da rawarsu, babu wani mai goya musu baya face wadanda za su amfana daga rikicin da za su jefa yankin ciki. Idan kuma suka ki yi wa kansu karatun ta nutsu, kasar Sin ta riga ta bayyana matsayarta na kin amincewa da duk wani yunkuri na ballewa, abun da ke nufin Taiwan za ta dandana kudarta idan ta bijire.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp