A jiya Talata ne aka gudanar da taron majalisar shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 23, inda aka fitar da sanarwa game da yaki da ta’addanci, rarrabuwar kawuna da tsattsauran ra’ayi da kuma hadin gwiwa a fannin sauye-sauye na zamani.
Sanarwar da aka fitar kan yaki da tsattsauran ra’ayi da ke haifar da ta’addanci, da wariyar launin fata, ta jaddada cewa, kasashe mambobin kungiyar sun kuduri aniyar kara zurfafa aiwatar da doka da hadin gwiwar tsaro a cikin kungiyar, da inganta hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa hadin gwiwa a matakin duniya, shiyya-shiyya da kasa, da tabbatar da daidaito ta bai daya. Da cikakken haÉ—in kai da tsaro mai dorewa, da daidaita martani ga barazanar tsaro da kalubale na cikin gida da na waje.
Haka kuma, sanarwar da aka fitar kan hadin gwiwa a fannin sauye-sauyen zamani ta ce, sauyi zuwa fasaha ta zamani wani karfi ne na ci gaban duniya, hade da ci gaba mai dorewa, kuma yana da amfani wajen cimma burin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta 2030. (Yahaya Yaya)