Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da hana su faɗar albarkacin baki.
A cikin wata wasiƙar da suka aike wa shugaban ƙasa ranar 20 ga Satumba, 2025, SERAP da Amnesty sun bayyana cewa ƙarar da DSS ta shigar bisa zargin saƙonnin da ake cewa sun na adawa da Tinubu ya zama wani SLAPP (ƙarar da ake amfani da ita don toshe bakin masu suka). Sun ce irin waɗannan suna haifar da tsoro da hana ƴancin faɗar albarkacin baki da musayar bayanai a cikin al’umma.
- Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
- DSS Ta Ba Sowore Mako Ɗaya Ya Janye Maganarsa Kan Tinubu
Ƙungiyoyin sun buƙaci shugaban ƙasa ya umarci Ministan Shari’a kuma AGF, Lateef Fagbemi (SAN), ya gaggauta janye ƙarar tare da gabatar da dokar hana SLAPP a gaban majalisar dokoki. Sun ce hakan zai kare ƴan ƙasa daga amfani da kotu wajen take ƴanci tare da tabbatar da ƴancin faɗar albarkacin baki da suka ce ginshiƙi ne na kowace dimokuraɗiyya.
Sun kuma yi gargadin cewa idan gwamnatin Tinubu ba ta janye ƙarar cikin kwanaki 7 ba, za su kai ƙarar gaban Kotun ECOWAS. SERAP da Amnesty sun jaddada cewa ƴancin faɗar albarkacin baki haƙƙi ne na kowa, kuma ƴan siyasa, musamman shugabanni, ya kamata su ɗauki suka da adawa a matsayin wani ɓangare na rayuwar dimokuraɗiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp