Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki na kasa mai zaman kanta (SERAP) ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ya yi watsi da bukatar gina wa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Gida na Naira biliyan 15 da aka ware a cikin karin kasafin kudin babban birnin tarayya (FCT).
Kungiyar ta ce, kudaden da ake shirin kashewa ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma alkawurran da kasar ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tallafa wa hakkin dan Adam a duniya.
- An Kammala Wasan Karshen Damben Warriors Na Wannan Shekarar A Kano
- Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista
A cewar mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, Majalisar Dattawa ce ke da alhakin tabbatar da dokar tsarin kashe kudade wacce kuma ta yi daidai da ka’idojin tsarin mulki, kuma dole dukkan jami’an gwamnati su kasance suna bin doka da oda.
Wasikar da SERAP ta aikewa shugaban majalisar dattawa a baya-bayan nan ta bayyana muhimmiyar rawar da majalisar ta taka wajen shawo kan matsalar basussuka da ke kara tabarbarewa a kasar.
Kungiyar ta bukaci majalisar dattijai da ta guji amincewa da duk wani almubazzaranci ko kashe kudaden da ba su zama dole ba da nufin inganta jin dadin jami’an gwamnati.