An bai wa Gianluigi Donnarumma jan kati kai tsaye minti 10 kacal da fara wasan Paris Saint-Germain (PSG) a gasar Ligue 1 a ranar Lahadi.
Mai tsaron ragar na kasar Italiya ya fito ne domin tare wata kwallo da mai tsaron ragar Kungiyar Le Havre ya bugo ta sama, amma sai aka samu akasi ya banke daya daga cikin yan wasan cikin kuskure.
Amma alkalin wasa Bestien Dechapy ya yanke shawarar nuna masa katin kora ba tare da bata wani lokaci ba, hakan yasa mai tsaron ragar kasar Spain Arnau Torres ya maye gurbinsa.
Talla