Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, ya musanta zargin da Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS), Comrade Atiku Abubakar Isah, ya yi masa na cewa ya sace shi kuma ya doke shi.
Isah ya yi iƙirari a wani taron manema labarai ranar Laraba cewa Seyi da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, sun ba shi cin hancin Naira miliyan 100 a Legas don ya tallafa wa shugaban ƙasa. Ya ce ya ƙi karɓar tayin saboda rashin tsinana komai da shugaban ƙasr yayi, kuma yace an sace shi, aka tuɓe shi tsirara, sannan aka doke shi tare da yi masa barazana a ranar 15 ga Afrilu.
- Sarkin Kano Na 15, Aminu Ado Bayero Zai Naɗa Ɗan Uwansa Sanusi Ado A Matsayin Galadiman Kano
- Tinubu Ba Ya Tsoma Baki A Ayyukan EFCC – Olukoyede
A cewar Isah, “An sace ni a ranar 15 ga Afrilu. An tuɓe ni tsirara kuma an doke ni sosai. Sun yi mini barazana cewa za su fitar da bidiyon. Sun ce ba za su fuskanci wani abu ba ko da sun fitar da bidiyon, ko ma idan sun kashe ni, Seyi Tinubu zai ba da umarnin a rufe lamarin.”
Duk da wannan bayanai, Seyi Tinubu ya ƙaryata duk waɗannan ikirari a wani rubutu a shafinsa na Instagram ranar Juma’a, yana mai cewa duk labarin ƙanzon Kurege be ne da aka yi niyya don bata masa suna. Ya bayyana cewa bai taɓa ganin Isah ba, balle ya tattaunawa da shi a ko’ina.
Ya ce, “Kai… mutum yana iya yin ƙarya da cikakkiyar ƙwarin gwuiwa? Wani yunƙuri ne na bata min suna. Allah ya taimake ka, Comrade Atiku Isah. Ban taɓa yin taro da Comrade Isah a Legas ko ko’ina a duniya ba. Ban taɓa ganinsa ba, kuma ban ziyarci wani wuri da ’yan daba ba. Duk waɗannan zarge-zargen da Atiku Isah ya yi labari ƙarya ne.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp