Darikar Confucius ta ƙayyade cewa “ya kamata mu nemi jituwa a cikin bambance-bambance kuma kada mu yi wa wasu abin da ba za mu so a yi mana ba”. Burin kasar Sin shi ne ta samar da daidaito a wannan duniyar da ke cike da bambance-bambance.
Duniyar tana daɗa dunkulewa waje guda tare da dogaro da juna, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin ƙasashe ta zama abu mai muhimmanci ga bunƙasar tattalin arziki, haɗin gwiwar duniya, da kwanciyar hankali na jama’ar duniya.
A kowace shekara, shugabannin gwamnatoci da galibin ministocin zartaswa na yin taro don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi ƙasa da ƙasa, da ƙarfafa amincewa da fahimtar juna. Shi ya sa wannan dabarar Amurka ta “de-risking” wato “a raba gari da Sin” ka iya haifar da sakamakon da bai dace da dabarun haɗin gwiwar da ake bukata ba. Kuma abin lura shi ne, ƙasar Sin ba kamar Amurka ba, Sin na da ikon samun wadata kuma tana baiwa sauran ƙasashen duniya damar ci gaba a cikin wadatar da ta samu.
Mu ɗauki harkallar Tesla a kasar Sin a misali, wani lamari ne mai muhimmanci. Maimakon hana Tesla walwala a kasuwan Sin – kamar yadda Amurka ta yi wa kamfanin Huawei kuma take ƙoƙarin yi wa Tiktok na Sin a maimakon haka, ta ba da yanayin kasuwanci mai kyau da kuma babbar dama ta kasuwanci ga babbar fasahar Amurka, wato kasancewar kamfanin Tesla a Sin wanda ya sanya ƙarin matsin lamba ga masana’antun motoci masu amfani da makamashin lantarki (EV) na cikin gida, amma hakan bai zama matsala ga ƙasar Sin ba saboda ta yi imanin cewa hajjar Sinawa da ta Amurkawa duk za su haɓaka kuma su yi nasara ta hanyar tsaftacciyar gasa. Idan da Sin ta kasance kamar Amurka ne, da kamfanoni irin su Apple, Microsoft, Boeing da Nvidia ba za su yi tasiri ko su samu nasara a babbar kasuwar duniya ba.
A bangaren siyasa kuma, rikicin siyasa a cikin Amurka ya kai wani mataki na tarihi —- ’yan jam’iyyar Democrat da Republican suna rashin jituwa kan kusan dukkanin manyan batutuwa, kamar yadda kacaniyar batun bashi na kwanan nan ya sake bayyanawa. Kuma wannan rikici ba kawai yana shafar jama’ar Amurka ba, har ma da sauran sassan duniya.
A cikin wannan zamani na canji da rashin daidaito, kwanciyar hankali da ci gaban ƙasar Sin na nufin wadata da samun kasuwa mai girma, da ƙarin jari, da damar zabin kayayyaki masu inganci, da ƙarin damar yin haɗin gwiwa. Daga shekarar 2013 zuwa ta 2021, matsakaicin gudummawar da Sin ta bayar wajen ci gaban duniya ya haura da kashi 30 cikin ɗari, fiye da haɗin gwiwar kungiyar G7, kuma ta zama ta ɗaya a dukkan ƙasashe. Kasancewar ƙasar Sin kan gaba wajen tabbatar da haɗin kai wata albarka ce ga al’ummarta, amma kuma abin dogaro ga jama’ar sauran ƙasashe.
Amurka ta ayyana ƙasar Sin a matsayin abokiyar adawa yayin da ita ƙasar Sin ba ta da sha’awar ƙalubalantar Amurka game da tafiyar da lamurran da suka shafi ci gaban duniya, musamman fasahar zamani, kasuwanci da tattalin arziki. Tasirin Amurka a sauran ƙasashen duniya ne ke kara raguwa saboda tsarin siyasarta da bukatunta. Babu wanda za a zarga da sanyaya dangantakar Amurka da ƙasashen duniyar da ke adawa da irin tsarinta na “wariya da rarrabuwa” face zabin da Amurka ta yiwa kanta.
Kamar dai yadda Jeffrey Sachs, farfesa kuma darektan cibiyar raya ci gaba mai dorewa ta jami’ar Columbia, ya ce a dandalin dimokuradiyya na Athens 2022, ƙasar Sin ta samu nasarori masu ban mamaki a cikin shekaru 40 da suka gabata, don haka ya kamata mu “yi farin ciki da nasarorin da ƙasar Sin ta samu, ba wai mu tsorata ba.” (Yahaya Babs)