• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka

by Sulaiman
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A cikin shekaru 45 da suka gabata, tattalin arzikin ƙasar Sin ya samu bunƙasuwa sosai, inda ya zama na biyu mafi girma a duniya.

Ƙasar ita ce mafi girma a duniya wajen fitar da kayayyaki da kasuwanci ga yawancin ƙasashe. Sai dai har yanzu kuɗin ƙasar na RMB Yuan na baya wajen hada-hadar kasuwancin ƙasa da ƙasa.

  • Kasar Sin Ta Kara Samar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki A Qinghai

Ƙasar Sin ta sake tsallake wani mataki a yunkurinta na rage dogaro da dalar Amurka yayin da amfani da kuɗin Sin RMB Yuan wajen hada-hadar cinikayyar tsakanin ƙasashe a rubu’i na biyu na bana ya zarce kuɗin Amurka a karon farko. Kason kuɗin cikin gida na kuɗaɗen da ƙasar Sin ta biya a tsakanin ƙasashe ya ƙaru da kashi 49 cikin ɗari a karshen watan Yuni daga kusan sifili a shekarar 2010.

Kason dalar Amurka ya fadi zuwa kasha 47 cikin ɗari daga kashi 83 cikin ɗari a daidai wannan lokacin. Wannan gagarumar nasarar da aka samu ta nuna yadda ƙasar Sin ke samun bunƙasuwar tattalin arzikinta, da ƙaruwar tasirin kuɗinta.

Musamman ma, RMB Yuan ya tashi daga matsayinsa na 35 a shekara ta 2001, ya zama na biyar mafi yawan kuɗin da aka fi ciniki da shi a duniya. Har ila yau, ya inganta a matsayi kuɗin kashewa a duniya, a halin yanzu yana matsayi na biyar bayan dalar Amurka, Euro, Fam na Birtaniya, da Yen Japan. Wanda ya kasance a matsayi na 30 a shekara ta 2011.

Labarai Masu Nasaba

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun nuna cewa an canza matsayin dala daga hanyar hada-hadar kasuwanci da musayar fasaha zuwa makamin siyasa. Sakamakon haka, ƙasashe da yawa sun zaɓi rage hannun jarinsu a cikin lissafin baitulmalin Amurka, sun zabi sarrafa kadarorinsu ta hanyar haɓaka ajiyar zinariyarsu. Har ila yau, sun zaɓi gudanar da kasuwancinsu tsakanin sauran ƙasahse ta hanyar amfani da kuɗaɗen cikin gida.

Mu dauki Rasha a misali, ba ta da wani zaɓi illa ta fara amfani da wasu kuɗaɗe wajen cinikin kasa da kasa. Ta fara karɓar kuɗaɗen man fetur, iskar gas, da kwal a yuan, sa’an nan Moscow ta ƙara yawan hannun jarinta na RMB Yuan a asusun ajiyarta na waje.

Manyan kamfanonin Rasha, irin su Rosneft, sun ba da lamunin RMB RMB Yuan. A cewar Bloomberg, RMB Yuan yanzu ya zama mafi yawan kuɗin hada-hadar kasuwanci a Rasha.
Bayan da ƙasar Rasha ta fara amfani da kuɗin Yuan sosai, wasu ƙasashe sun fahimci alfanun da ke tattare da hakan, kuma sun ga wata dama ta rage dogaro da dalar Amurka, lamarin da ya haifar da sarkakiya.

A farkon wannan shekara, Beijing ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin ƙasashen biyu da Brazil don samar da waken soya. Yarjejeniyar na ba da damar musayar kai tsaye tsakanin Yuan da Real ta Brazil. A watan Afrilu, Argentina ta ba da sanarwar sauya sheka daga amfani da dala zuwa yuan wajen shigo da kayayyaki daga Sin.

Indiya na amfani da kuɗaɗen da ba na dalar Amurka ba, irin su Dirhami na UAE da Ruble na Rasha, don biyan mafi yawan kuɗin man Rasha da suke shigo da su. Hakazalika, Bangladesh ta fara biyan Rasha da yuan kuɗin gina tashar makamashin nukiliya. Iraqi na da niyyar amfani da yuan a matsayin kuɗin biyan kayayyakin da take shigo da su daga Sin. Faransa ta amince da yuan a matsayin biyan kuɗin iskar gas da aka saya daga wani kamfanin mai na ƙasar Sin.

A cikin wani rahoto da aka wallafa a mujallar Time, ministan tattalin arziki da kuɗi na jama’ar Bolivia Marcelo Montenegro ya ce “Mun riga mun fara amfani da yuan. Gaskiya ne kuma kyakkyawan farawa … masu fitar da ayaba, zinc, da itace, suna gudanar da hada-hadar kuɗi a yuan, da masu shigo da motoci da manyan kayayyaki.”

An kuma bayyana cewa, a tsakanin watan Mayu da Yuli na bana, Bolivia ta yi hada-hadar kuɗi da ta kai kuɗin Sin yuan miliyan 278, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 38.7, wanda ya kai kashi 10 cikin 100 na cinikin ƙasashen waje. Ban da wannan kuma, ƙasar Sin ta zama abokiyar cinikayya ta biyu mafi girma a ƙasar Bolivia, kuma babbar hanyar shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, kuma haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu ta shafi bangarori daban-daban, da suka haɗa da kayayyakin more rayuwa, da harkokin sararin samaniya, da fasahar watsa labaru, da raya mai da iskar gas. Ta kuma yi la’akari da yiwuwar amfani da kuɗin kasar Sin wajen biyan basussukan da asusun lamuni na duniya IMF ke bin ta.

Ana sa ran taron BRICS mai zuwa da za a yi a cikin watan Agustan nan a Afirka ta Kudu, zai tattauna kan aikace-aikace daga ƙasashe masu tasiri da dama da ke neman shiga ƙungiyar. Yanzu an lura cewa mahalarta taron suna shirye don tallafawa gabatar da kuɗi mai zaman kansa a madadin dalar Amurka.

Daga cikin masu neman wannan matsayi har da kuɗin Yuan, tun da yawan GDPn ƙasar Sin ya kai kashi 71 cikin 100 na adadin da ake ciki yanzu.

Yayin da takarar tasirin darajar kuɗi ke kankama, bari mu ari kalaman wani babban dan wasan hockey Wayne Gretzky da ya ce, “a maida hankali a inda kwallon zai sauka, ba inda kwallon yake ba.” Lallai tasirin kuɗi a hada-hadar kasuwancin duniya ya baro dalar Amurka yayin da yuan na kasar Sin ke shirin tumbuke dalar ta Amurka. (Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dakarun Sojin NijeriyaDalar Amurka
ShareTweetSendShare
Previous Post

Amurka Ta Kasa Tilastawa Kasashen Afirka Su Goyi Bayanta

Next Post

Ministoci: Majalisar Dattijai Ba Ta Tabbatar Da Tantance Elrufai, Okotete Da Danladi Ba

Related

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu
Daga Birnin Sin

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

4 hours ago
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

6 hours ago
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow
Daga Birnin Sin

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

6 hours ago
Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare
Daga Birnin Sin

Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

18 hours ago
Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali
Daga Birnin Sin

Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

19 hours ago
Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani
Daga Birnin Sin

Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

20 hours ago
Next Post
Ministoci: Majalisar Dattijai Ba Ta Tabbatar Da Tantance Elrufai, Okotete Da Danladi Ba

Ministoci: Majalisar Dattijai Ba Ta Tabbatar Da Tantance Elrufai, Okotete Da Danladi Ba

LABARAI MASU NASABA

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 9, 2025
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

May 9, 2025
Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.