A ranar Juma’a ne kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICJ) wanda aka fi sani da kotun duniya ta ba Isra’ila umarni guda shida dangane da kisan kiyashi da take yi a Gaza, amma babu batun tsagaita bude wuta a cikin umarnin a bayyane.
An sanar da matakin na gaggawa ne a daidai lokacin da kotun ta yi zama kan shari’ar kisan kiyashin da kasar Afirka ta Kudu ta shigar a kan Isra’ila, wanda ta saurari shaidu a farkon wannan watan. Afirka ta Kudu ta bayyana abin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza a matsayin kisan kare dangi amma Isra’ila ta musanta zargin, tana mai cewa yakinta a Gaza ya samo asali ne daga yunkurin “kare kai”, kuma ya zama dole ta kawar da Hamas. Ta kuma jaddada cewa ba za ta kawo karshen yakin ba har sai ta cimma wannan buri.
- Micheal Keating: Kasar Sin Ba Barazanar Tattalin Arziki Ba Ce
- Masana’antun Kauyukan Sin Sun Samu Ci Gaba Yadda Ya Kamata A Shekarar 2023
Kusan watanni hudu ke nan duniya tana kallon yadda ake ruguza Gaza, lamarin da ya haifar da rikicin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba. Ba a taba ganin irin wannan zaluncin da gangan ba a duniya, tare da nuna kyama ga kimar dan Adam da rayuwar dan Adam, yayin da wasu daga cikin manyan kasashen duniya suka ci gaba da siyasantar da batun.
Kotun duniya ta yi umarni ga Isra’la kamar haka, dole ne Isra’ila ta dauki duk matakan da za a iya dauka don hana aikata abubuwa kamar yadda aka zayyana a cikin mataki na 2 na yarjejeniyar hana kisan kare dangi ta 1948. Wanda ya kunshi hana kashe mambobin wata kungiya, hana haifar da cutarwa ta jiki ko ta hankali ga mambobin wannan kungiyar, hana haifar da yanayin rayuwa wadanda za su kai ga kawo karshen wanzuwar wata al’umma, da kuma hana aiwatar da ayyukan da aka tsara don hana haifuwa a cikin wannan rukunin mutane. Dole ne Isra’ila ta tabbatar da cewa sojojinta ba su aiwatar da ko daya daga cikin wadannan matakan ba ga Falasdinawa ba.
Umarnin ya ci gaba da cewa, dole ne Isra’ila ta hana tare da hukunta wani tunani ko jama’a da suka shirya yin kisan kare dangi dangane da mambobin kungiyar Falasdinu a zirin Gaza”. Dole ne Isra’ila ta tabbatar da isar da muhimman ayyuka da kuma muhimman kayan agajin jin kai ga fararen hula a Gaza. Dole ne Isra’ila ta hana lalata shaidun laifukan yaki a Gaza tare da ba da damar gudanar da bincike na gaskiya. Dole ne Isra’ila ta gabatar da rahoto kan duk matakan da ta dauka don yin biyayya ga matakan da kotun ta dauka a cikin wata daya da yanke hukuncin.
To tambayar ita ce, shin Isra’ila za ta yi biyayya ga kotun duniya dangane da wannan hukunci? Tuni dai Isra’ila ta halaka Falasdinawa sama da 26,000 a hare-haren da take kaiwa kan zirin Gaza. Tare da katse hanyoyin sadarwa, da ta samar da abinci da agajin jin kai, da magunguna da ruwan sha. (Muhammed Yahaya)