Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sun isa kotun kolin Nijeriya a yau Juma’a domin sauraren hukuncin karshe kan zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa za a raba gardama tsakanin Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP da babban abokin hamayyarsa a zaben, Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
- Shiriya, Ni’ima Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW)
- Malam Isa Gusau, Jami’in Yaɗa Labarai Na Gwamna Zulum Ya Rasu
Kotun koli ta tsayar da ranar Juma’a 12 ga watan Junairu, 2024 domin yanke hukunci kan karar da gwamna Yusuf ya shigar kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya, na tsige shi daga kujerar gwamnan jihar.
LEADERSHIP ta hangi wasu gwamnonin jihohin da su ma za a yanke hukunci kan shari’ar zaben jihohinsu.
Gwamnonim sun hada da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da takwaransa na Jihar Zamfara, Dauda Lawal.
A yau Juma’a ne ake sa ran kotun koli za ta yanke hukunci game da rikicin zaben gwamnoni takwas.