Maza da mata da sun fito kan titunan Kano domin murnar hukuncin da kotun koli ta yanke na ayyana gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar.
Kanawa sun yi dafifi a tituna jihar, suna rera wakoki, kade-kade da raye-raye don nuna farin cikinsu.
- Kotun Koli Ta Ayyana Muftwang A Matsayin Halastaccen Gwamnan Filato
- Shari’ar Kano: Gwamna Yusuf Da Mataimakinsa Sun Halarci Zaman Kotun Koli
Da yake zantawa da LEADERSHIP, wani mazaunin Soron Dinki da ke cikin birnin Kano, Mahdi Yusuf, ya nuna jin dadinsa da hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ya ce hakan ya kawar da tashin hankali a jihar.
“Kotun koli ta ceci Kano daga tashin hankali, domin da a ce hukuncin ya zama akasin haka, da ko jami’an tsaro ba za su iya shawo kan lamarin ba.
“Amma yanzu an samu kwanciyar hankali. Jama’a sun fito suna murna saboda farin ciki,” in ji shi.
An rufe kasuwanni tun da sanyin safiyar Juma’a saboda fargabar barkewar tashin hankali.
A baya dai rundunar ‘yansandan jihar ta yi gargadi kan tashin hankalin da ka iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
A halin da ake ciki, an tsaurara matakan tsaro a dukkanin hanyoyin zuwa gidan gwamnatin Kano, yanzu haka cincirindon mutane na jiran isowar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf daga Abuja.