Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bai wa jam’iyyar PDP wa’adin kwana 10 don warware rikicin cikin gida tare da rushe taron zaɓen da aka yi kwanan nan a Ibadan da kuma kafa kwamitin riƙon ƙwarya na ƙasa.
Lamido ya yi kiran a ranar Alhamis yayin da yake magana ga goya bayansa ciki har da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi da tsofaffin kwamishinoni, da sauran shugabannin siyasa da aka naɗa wanda suka kai masa ziyara ta zumunci a ofishinsa na Sharada a Kano.
- Shugabannin APC Da PDP Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Gwamna Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Ya bayyana damuwa game da rikicin da ke ci gaba da ruruwa a cikin jam’iyyar, yana mai cewa masu ruwa da tsaki na da dogon lokaci na warware matsalar PDP.
Ya jaddada cewa matakan shari’ar da ya ɗauka ba don an haka masa tikitin takarar shugaban jam’iyyar ba ne, amma don ya kare muradun PDP da haƙƙinsa da aka take.
Ya dage cewa, a halin da ake ciki, Umar Damagum da Samuel Anyanwu suna nan a matsayin sahihan shugabannin jam’iyyar har zuwa lokacin da wa’adinsu zai kare a ranar 8 ga Disamba, 2025.
Ya yi gargaɗin cewa barin jam’iyya ta ci gaba ba da tafiya a haka ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba ga makomar masu neman muƙamai, masu riƙe da ofisoshi, da waɗanda ke shirin sake tsayawa takara.
Tsohon gwamnan ya yi kira ga shugabannin PDP su shirya taro na haɗin gwiwa don su fuskanci ƙalubalen jam’iyyar da gaskiya tare da mayar da ita zuwa matsayinta na gaskiya a siyasar ƙasar nan.
Har ila yau, ya buƙaci goya bayansa da su kasance cikin natsuwa da haƙuri har zuwa 8 ga Disamba don ganin yadda abubuwa za su kasance.














