Wato manufar wannan rubutu ita ce, ina so na zama uba da uwa ga matasanmu marasa iyaye, da kuma wanda ba su samu damar koyar rayuwa daga wajen iyayensu ba.
Abin bakin ciki al’ummar mu ta fi mai da hankali wajen yi wa mata fada da gyara, akan manta da maza. Shi ya sa lokaci zuwa lokaci nake rubuce-rubuce don na fadakar ko na wayar da kan matasa maza. Yau za mu tattauna akan wani batu: Wato idan matarka ta samu Juna biyu.
- Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu
- Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin
Wani dan-uwa ya ce, Ya Muhammad, matata ta samu juna-biyu, kuma tun da ta samu, bama samun damar shiga “dakiñ canba”. Ya nuna damuwa sosai, kuma a matsayina na gogyaggye zan yi bayani akai zan kira ka don mu tattaunawa. Kuma Alhamdu lillah, na kira shi, kuma ya ji dadi sosai, kuma ya fahimci sakon. Na ce duk da haka ya kamata a wayar da kai don kar a bar ‘yan baya.
Ya kai matashi, yana da kyau ka sani. Ita mace a duk sanda ta samu juna-biyu, wannan lokaci, shi ne lokaci mafi wuya da kalubale a wurinta. Allah ne ya tsara haka, ka ga mace ta shiga wani mawuyacin hali musamman a wata ukun farko, wato tana cikin watanni uku na farko.
A wannan lokaci za ka lura cewa ba ta son abubuwa da yawa, kai wata ko kamshin turarenka ba ta so. Wata ko kusa da ita ba ta so ka zo. Sannan za ta yi ta rashin lafiya da son kwanciya. Wata sai ta yi kamar za ta mutu, ka ga ta kyar take iya tashi. Sannan shi kansa kauracewa kwanciya a wannan lokacin zai iya zama alkhairi.
Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo na musamman.
Idan kaga wannan lokacin yazo, anan ne ake so ka nuna soyayyarka, da kulawarka, da taimakonka. Wajibi ka bata hadin-kai don ta wuce wannan watanni uku na farko din. Domin cikin jikinta a wannan lokacin kamar akan siratsi yake, duk abinda aka ce ana halittarta ’yan Adam a cikinsa ai yaga taka kansa. Komai zai iya faruwa. Namiji dan kirki shine sai kaga ya shiga kokarin yin hidimar gida da kansa. Shine wanke wanke, shara, girki, kaye kaye da sauransu. Sannan duk abinda tace tana sha’awa indai da hali a saya mata. Wallahi ba daga ita bane, daga yanayin cikin ne. Za Mu Ci Gaba Mako Mai Idan Allah Ya Kai Mu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp