Abokaina, ko kun taba kai ziyara a tashar jiragen ruwa ta Lekki dake Legas, Najeriya? Wata sabuwar tashar zamani ce, da Najeriya da Sin, da sauran bangarorin kasa da kasa, suka gina a hadin gwiwarsu, wadda ta kasance tashar jiragen ruwa mafi girma ta Najeriya. Ban da haka, bisa matsayinta na tasha mai kunshe da mafi yawan fasahohin zamani a yammacin Afirka, tashar jiragen ruwa ta Lekki na taka rawar gani a fagen zamanantarwa da ci gaban tattalin arzikin Najeriya, da na sauran kasashe makwabtanta. Sai dai idan an tantance dalilan da suka haifar da tashar, za a ga akwai tallafin da aka samu daga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) da kasar Sin ta kaddamar.
Akwai dimbin abokai da suka yi mana tambaya kan ma’anar taken shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Hakika wannan suna yana da alaka da muhimman tsoffin hanyoyin ciniki da suka hada kasar Sin da sauran kasashe a tarihi, wato Hanyar Siliki, da Hanyar Siliki dake Kan Teku. Dalilin da ya sa aka ba wata sabuwar shawara sunan wasu tsoffin hanyoyi, shi ne domin muhimmiyar rawar da tsoffin hanyoyin suka taka ta fuskar raya tattalin arzikin duniya, inda a maimakon dogaro kan karfin makamai, da kaddamar da yaki, aka yi amfani da ayarin rakuma, da jiragen ruwan dakon kaya, wajen karfafa cudanyar ciniki, da al’adu, tare da tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban.
Shawarar BRI ta gaji ruhin tsoffin hanyoyin ciniki da aka kafa a tarihi, inda ta samar da damammaki na samun ci gaba ga duniya, abin da ya sa ta samun karbuwa sosai. Idan muka dauki nahiyar Afirka a matsayin misali, tun bayan da kasar Sin ta kaddamar da shawarar BRI a shekarar 2013, har zuwa yanzu, kasashe 52 dake nahiyar Afirka da kwamitin kungiyar kasashen Afirka ta AU, dukkansu sun kulla yarjeniyoyi na hadin gwiwa tare da kasar Sin, a karkashin shawarar. Ta haka, an samu dimbin sakamako masu gamsarwa, inda a fannin ciniki aka samu ci gaba sosai, ko a shekarar bara kadai ma, yawan cinikin da kasar Sin ta yi tare da kusan rabin kasashen dake nahiyar Afirka ya karu da fiye da kaso 10%. Bayan haka, kasar Sin ta zama kasar da ta zuba mafi yawan jari ga kasashen Afirka, kana a cikin shekaru 3 da suka wuce, kamfanoninta suka samar da guraben aikin yi fiye da miliyan 1 da dubu dari ga kasashen Afirka. Haka zalika, an gina dimbin kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka, bisa hadin gwiwa da kasar Sin.
Sai dai ta yaya za a iya tabbatar da cewa, BRI za ta ci gaba da haifar da alfanu ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki? A jiya Litinin, an gudanar da taron karawa juna sani kan aikin aiwatar da BRI karo na 4 a birnin Beijing na kasar Sin, inda shugaban kasar Xi Jinping ya bayyana tsarin da za a bi wajen ci gaba da aiwatar da shawarar BRI a nan gaba. Cikin jawabinsa, ya yi bayanai masu muhimmanci, kamar su “kokarin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya” da “tsayawa kan manufar tattaunawa tare da kasashe daban daban, da yin aiki bisa hadin kai tare da su, gami da raba damar cin moriya tare da su”, da dai makamantansu. Abin lura shi ne, wannan taro na manyan jami’an kasar Sin ne, maimakon na kasa da kasa, don haka, maganar da shugaba Xi ya fada, ba da umarni ne ga jami’an Sin, maimaikon tallar wata manufar Sin ga kasashe daban daban. Amma duk da haka, shugaban na kasar Sin bai taba nuna son kai ba ko kadan. Kafin ya ambaci batun kare moriyar kasar Sin, ya jaddada bukatar samar da karin alfanu ga kasashen da suke cikin shawarar BRI.
A ganina, zamanin da muke ciki ya baiwa BRI karin muhimmanci. Saboda a halin yanzu, an fi nuna ra’ayi na son kai a duniyarmu, inda dimbin kasashe ke son daukar matakan radin kai, da bata huldar ciniki, da kin dunkulewar tattalin arzikin duniya. Sai dai duk da haka, BRI na ci gaba da samar da wani yanayi mai yakini a duniya, inda take kokarin tabbatar da samun zaman lafiya, da hadin kai, da kare moriyar bangarori daban daban, da neman samun ci gaba tare. (Bello Wang)