• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarar Tabbatar Da Tsaron Duniya: Sin Ta Zo Da Mafita Ga Alkaba’in Tashe-tashen Hankula

byAbdulrazaq Yahuza
1 year ago
Tsaron

Ko dan jariri da ke cikin mahaifiyarsa ya san irin alkaba’in da ke addabar duniya a halin yanzu ta fuskar tabarbarewar tsaro.

Tsoro da firgici na ci gaba da haifar da razani a tsakanin al’umma. An mayar da kwararar da jinin Bil’adama ba a bakin komi ba.

  • Kotu Ta Tsare Mutane 29 Masu Rajin Kafa Kasar Yarbawa A Oyo
  • Wata Kungiya Ta Shirya Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi 400,000 A Nijeriya

Ana kashe mata da kananan yara, haka nan tsofaffi da dattawa duk babu wanda ya tsira. Dokokin kiyaye kisan kare-dangi tamkar ba su aiki saboda munafurcin Turawan yamma. Wanda suke so shi ne da gaskiya komai zaluncinsa wanda ya zamo dan adawarsu kuwa shi ne tunku-uwar-laifi duk irin gaskiyarsa.

Tauye ‘yancin kasashe masu cin gashin kansu ya yawaita, karfafa abokan hulda masu tayar da zaune tsaye a kasashen da suka ki bayar da kai bori ya hau ya zama ruwan dare game da duniya. Duk wadannan abubuwa an gan su a Zahiri sun faru a Iraki, Libiya, Benezuela da wasunsu da dama. Sai kuma rikicin cikin gida da ake rurawa da kusan yau a duniya kasashe daidai ne suka tsira daga makircin su Amurka kan haka.

Al’ummar duniya ta gaji da alkaba’in rashin tsaron da ake fama da shi, wanda wani lokaci mutumin da yake rayuwa a doron kasa musamman a yankunan da abin ya fi kamari yake burin ina ma shi ne a cikin kabari. Kazantacciyar zubar da jinin da ake yi a yankin Gaza tun daga watan Oktobar bara zuwa yau ya isa abin misali baya ga rikicin da ya zama kamar cin kwan makauniya irin na Somaliya ko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sannan ga wanda ake fama da shi a tsakanin Rasha da Ukraine. Tambayar da kowa ke yi ita ce, yaushe masu haddasa wannan husuma za su bar al’ummar duniya ta numfasa?

LABARAI MASU NASABA

Bitar Aikin Hajjin 2024

Sarkin Lafiya Ya Hada Kan Sarakunan Nasarawa Ba Bambanci – Zanwa

Mai karatu, na ci karo da wata kwakkwarar amsa a yayin da na samu labarin shawarar da kasar Sin ta gabatar mai taken Yunkurin Tabbatar da Tsaron Duniya, wadda Shugaba Di Jinping ya ambata a jawabinsa na bude taron Dandalin Boao, ranar 21 ga watan Afrilun 2022.

Wannan shawara cikin hikima da basira tana nuna matsayin kasar Sin na neman samar da ingantaccen tsaro mai amfanarwa tare da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Kasar Sin ta ba da shawarar kafa sabuwar hanyar tsaro bisa manufar tabbatar da tsaro na bai daya, da zai zama cikakke bisa hadin gwiwa wanda zai dore tare da mutunta juna a matsayin babban ginshiki. Haka nan shawarar tana neman a samar da wani tsari da zai sanya rashin rarraba tsaro a matsayin muhimmiyar ka’ida, da sanya burin samar da al’umma mai cikakkiyar tsaro a gaba.

Karin wani abin sha’awa game da wannan shawarar ta Yunkurin Tabbatar da Tsaron Duniya da kasar Sin ta gabatar shi ne, yadda ta kawo maslaha da tattaunawa da hadin gwiwa a matsayin mafita a maimakon amfani da adawa ko kawance na taron dangi.

Alamu sun nuna wannan shawara za ta samu nasara bisa yadda kasashe fiye da 100 da kungiyoyin yanki da na kasa da kasa suka yi na’am da ita tare da shigar da ita cikin kundayen huldar da ke tsakaninsu da kasar Sin, inda hakan ya sa ta zama abu mai muhimmanci ga sha’anin tsaron duniya.

Wannan tsari da shawarar ta kawo ya sha bamban da irin na kasashen yamma kamar su Amurka da ya jefa mu cikin alkaba’in tashe-tashen hankulan da muke gani a duniya. A tsarin tsaron su Amurka, kansu kawai suka sani ba ruwansu da saura da yi wa abin tanadi na fitar hankali kamar yadda Amurka ta ware Dala biliyan 886 a kasafinta na 2024 a fannin soja kawai. Wannan adadi da ya karu da kimanin Dala biliyan 30 a kan na bara, ba a taba ganin irin sa a tarihin kasar ba.

Har ila yau, sun hana duniya zaman lafiya domin kare muradun kansu ta hanyar kirkiro da kawance na soji daban-daban masu rarraba kawunan kasashe da kakaba takunkumai na karya tattalin arziki da tauye hakkoki da muradun kasashe wadanda dokokin duniya suka halatta da kuma zama kanwa uwar gami na wargaza sha’anin tsaron kasashe kamar yadda muke gani a Palasdinu da Tekun Kudancin Sin da Yankin Koriya.

Wannan ya sa nake da yakinin shawarar tabbatar da tsaron duniya da kasar Sin ta gabatar za ta wanzar da adalcin da ake fatan gani da zai zama silar magance alkaba’in duniya da kawar da tarnakin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasashe.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsaron
Sharhi

Bitar Aikin Hajjin 2024

December 30, 2024
Sarkin Lafiya Ya Hada Kan Sarakunan Nasarawa Ba Bambanci – Zanwa
Sharhi

Sarkin Lafiya Ya Hada Kan Sarakunan Nasarawa Ba Bambanci – Zanwa

May 17, 2024
Next Post
Me Ke Sa Wasu Maza Rashin Tsafta?

Me Ke Sa Wasu Maza Rashin Tsafta?

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version