Firaministan kasar Hungary Orban Viktor, ya yi kira a gun taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa karo na 3 na shawarar “ziri daya da hanya daya” da aka rufe ba da dadewa ba, da a darajanta layin dogon dake tsakanin Hungary da Serbia, kuma ya yi kira ga Turai, har ma duniya baki daya, da su fidda sabon zarafin kara tuntubar juna. Ya ce kara tuntubar juna zai samarwa Turai damar farfado da karfin takarar ta.
Tuntubar juna da Orban Viktor ya ambata muhimmin aiki ne a shawarar, kuma jigon wannan taro ne. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a bikin bude taron da aka yi a ran 18 ga wata, inda ya sanar da goyon bayan manyan ayyukan 8 na shawarar, aiki na farko daga cikinsu shi ne kafa tsarin tuntubar juna. Abin da ya nuna cewa, shawarar na mai da hankali matuka kan tuntube juna da hadin kai. (Amina Xu)