• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Riba Ce Ga Kasashe Masu Tasowa

by CMG Hausa
3 years ago
Ziri daya

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da nazari, da fafutukar neman kyakkyawar makoma a wannan mawuyacin lokaci da duniya take ciki, musamman ta fuskar koma bayan tattalin arziki, da gurguncewar sassa daban daban na ci gaba, sakamakon bullar annobar COVID-19, da rikicin kasar Ukraine da suka haifar da mummunar illa ga duniya, a hannu guda, kasashe musamman masu tasowa, na da kyakkyawan fatan samun ci gaba da wadata, karkashin ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa, bisa shawarar nan ta Ziri Daya da Hanya Daya wadda kasar Sin ta gabatarwa duniya.

Cikin irin wadannan ayyuka da a yanzu haka ke daf da kammala, akwai ginin tashar teku mai zurfi ta yankin Lekki na jihar Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya, wadda kasar Sin ta tallafa wajen gudanarwa.

  • An Shirya Tattaunawar Tiangong Tsakanin ‘Yan Sama Jannatin Sin Da Matasan Afirka Cikin Nasara

’Yan Najeriya da dama, da masana tattalin arziki a kasar, na jinjinawa kasar Sin, bisa aiwatar da wannan muhimmin aiki mai tarin alfanu, wanda zai fadada damar Najeriya ta karbar manyan jiragen dakon kayayyaki daga sassan duniya daban daban.

Aikin wanda zai lashe tsabar kudi har dalar Amurka biliyan 1.5, a yanzu ya kai kaso 95 bisa dari na kammala, ana kuma sa ran gama shi baki daya zuwa karshen shekarar nan ta 2022. Tashar za ta hade da yankin ciniki cikin ’yanci na jihar ta Lagos.

Da zarar tashar ta kammala, za ta zamo ta 3 da Najeriya ke da su, baya ga tsoffin tashoshin ruwa masu karbar jiragen ruwa guda biyu dake fama da cinkoso.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Sabanin tsofannin tashoshin biyu, sabuwar tashar teku mai zurfi ta Lekki, za ta iya karbar kayan da yawansu zai kai na sama da manyan sundukan dakon kaya masu fadin kafa 20 har miliyan 2.7 a duk shekara, kana tashar tekun mai zurfi, za ta samarwa Najeriya zarafin karbar sundukan dakon kayayyaki daga 3,000 zuwa 20,000 a kullum, wanda hakan ya sanya tashar zama daya daga ayyuka mafi muhimmanci da Najeriya za ta ci gajiyar su, karkashin shawarar Ziri Daya da hanya Daya.

Ko shakka babu wannan muhimmin aiki ne da zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta fuskar samun karin haraji, da guraben ayyukan yi, da fadada damammaki na kasuwanci da cinikayya, baya ga rage tsadar kudaden fito, da kara zamanintar da salon ba da hidimomin shige da fice da tashar za ta yi a kasa irin Najeriya, wadda ita ce mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afirka. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
PDP Ta Koka Kan Yadda Jami’an CJTF Ke Cin Zarafin ‘Ya’Yanta A Borno

PDP Ta Koka Kan Yadda Jami'an CJTF Ke Cin Zarafin 'Ya'Yanta A Borno

LABARAI MASU NASABA

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.