Yanzu haka shawarar “ziri daya da hanya daya”, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ta cika shakaru 10 da kafuwa. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan batun zuba jari a fannin kayayyakin more rayuwa, da harkar ilimi, da gine-gine, da samar da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da bil-Adam ke matukar bukata.
Alkaluma sun nuna cewa, shawarar ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, wadanda suka taba rayuwar al’ummomi masu tarin yawa, musamman a kasashe masu tasowa da dama.
- Yadda Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Jagoranci Aikin Raya Lardin Zhejiang
- Tunanin Gina Al’ummar Duniya Mai Makomar Bai Daya Ya Haskaka Makomar Duniya
Daga lokacin da aka gabatar da ita zuwa wannan lokaci, shawarar ta yi nasarar magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki a yankin Asiya da Fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai.
Masana sun yi imanin cewa, duk da yadda wasu kasashen yammacin duniya suka yiwa shawarar bahaguwar fahimta, shawarar “ziri daya da hanya daya” tana da muhimmanci wajen bunkasa alakar kasa da kasa. Kuma yanzu haka, akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa masu tarin yawa da suka sanya hannu kan shawarar.
Saboda muhimmanci da tasirin da shawarar ke kara yi a sassan duniya, yanzu haka an sanya shawarar cikin muhimman takardun manyan hukumomin kasa da kasa misali, MDD, da kungiyar G20, da kungiyar raya tattalin arzikin Asiya da Fasifik da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauransu.
Bugu da kari, duk da sauye-sauye da yanayi na rashin tabbas da ra’ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra’ayi na kashin kai da duniya ke fuskanta a halin yanzu, shawarar da kasar Sin ta gabatar, wata dama ce da sauran kasashe za su amfana da irin ci gaba da ma fasahohin da kasar Sin ta samu.
Shawara ce da ke mutunta ra’ayoyi da ka’idojin kasashe da tuntubar juna da alaka ta samu nasara tare gami da nuna daidaito. Haka kuma shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gabanta da sauran kasashen Afirka masu tasowa. Bayanai na nuna cewa, tun bayan da aka gabatar da shawarar, ya zuwa yanzu kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka’idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa. Ksar Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni.
Wannan yana kara shaida cewa, ya kamata a yi hadin gwiwa da samun moriyar juna da adalci da wadata tare, wanda zai taimaka ga ci gaban sassan duniya baki daya. Kuma Sin za ta ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban, don sa kaimi ga raya shawarar “ziri daya da hanya daya” da bayar da gudummawa ga samun ci gaba da wadata na bai daya a duniya
Bugu da kari, shawarar wani shiri ne da kasar Sin ta gabatar bisa buri guda da al’ummomin kasa da kasa ke da shi na samar da wadata ga duniya baki daya. A takaice dai shawarar ziri daya da hanya daya ta amfani al’ummar duniya.