Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya yaba wa rundunar ‘yansandan Nijeriya bisa kama wasu da ake zargi da kai wa ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a Jihar Borno.
Idan za a tuna cewa an kai wa ayarin motocin tsohon mataimakin shugaban kasa hari a Jihar Borno a yayin wani gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 10 ga watan Nuwamba.
- Baje Kolin Zuba Jari Ya Nuna Amincewar Duniya Game Da Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin
- Gwamna El-Rufai Ya Rantsar Da Sarkin Jere Na 11
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Borno, Abdul Umar, a ranar Alhamis, ya ce rundunarsa ta kama tare da gurfanar da mutum tara daga cikin maharan a gaban kotu.
Da yake mayar da martani, Shehu Sani ya yabawa ‘yansanda amma ya bukace su da su kara kaimi tare da tabbatar da cewa bata garin da suka kai hari a wurin taron shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna an kama su.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce, “Rundunar ‘yansanda ta kama tare da gurfanar da wadanda ake zargi da kai hari kan ayarin motocin Atiku Abubakar a lokacin da ya ziyarci Jihar Borno abin yabawa ne.
“Wadanda suka kai hari wurin taron dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Kaduna har yanzu ba a gurfanar da su gaban kuliya ba”.