Allah ya yi wa, Sheikh Awad Moawad Al-Subhi Al-Harbi, mai shekara 134 ya rasuwa a yau Asabar 10, ga watan Disambar 2022.
Sheikh Awad, yana daya daga cikin mutane maau tsawon rai a tarihi a kaf yankin Makkah.
- Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Limamin Madina Sheikh Abdurrahman Huzaify Rasuwa
- Sin Da Saudiyya Abokai Ne Na Gaskiya Bisa Manyan Tsare-tsare
Wasu sukan kira shi da “Tantabarar Masallaci” saboda halartar sallah a Masallacin Makkah da yake yi a koyaushe.
Shafin Haramain Sharifain da ke yada labaran da suka shafi masallatai biyu masu alfarma na Makkah da Madinah ne ya wallafa sanarwar rasuwar a yau.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kyauta bayansa da karshenmu,Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp