Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira da a janye takunkumin hana shigo da makamai da aka kakabawa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC).
A cewar wasu rahotanni, kungiyoyi masu dauke da makamai irin su M23, sun mallaki makamai na zamani fiye da jami’an tsaron DRC. A cewar Geng Shuang, wannan ya nuna mummunan tasirin da takunkumin kwamitin sulhu na MDD ya haifar kan karfin tsaron gwamnatin DRC, wanda ya saba manufar kwamitin game da kafa tsarin sanya takunkumi.
Ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kwamitin sulhun da ya soke butakar gwamnatin DRC sanar da shigo da makamai.
Ya zuwa wani lokaci, gwamnatin DRC tana ci gaba da inganta sauye-sauye a muhimman fannoni da ci gaba da inganta harkokin mulkinta, da samun ci gaba mai armashi wajen bunkasa tattalin arziki, da ciyar da tsarin zabe na shekarar 2023 gaba, da inganta ci gaban kananan hukumomi, da kwance damarar rundunonin soja.
Ya shaidawa kwamitin sulhun cewa, wadannan ci gaba da aka samu, suna karfafa gwiwa, kuma sun dace a kalle su da idon basira. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp