Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin Gummi, Bukkuyum da Maru.
Gwamnatin jihar ta zayyana jerin ayyuka da aka fi sani da ‘Ayyukan Ceto Zamfara’ don tunawa da shekara ɗaya na gwamnatin Dauda Lawal a kan mulki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta jaddada cewa an fara ƙaddamar da ayyukan ne da makarantar Tsangaya ta zamani da ke Ƙaramar Hukumar Gummi.
A cewarsa, an sanya wa makarantar Tsangayar sunan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III OFR, wanda ya kasance babban baƙo na musamman a wajen buɗe makarantar.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A yau ne gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗi a faɗin ƙananan hukumomin Zamfara 14 domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta ƙaddamar a shekarar da ta gabata.
“Ayyukan an sanya su a matsayin ayyukan ceto, waɗanda suka mai da hankali kan wuraren da ke ƙara darajar rayuwar al’umma, ciki har da tsaro, kiwon lafiya, ilimi, da kayayyakin more rayuwa da sauransu.”
Da yake gabatar da jawabinsa a ƙaramar hukumar Gummi, Gwamna Lawal ya jaddada cewa makarantar Tsangaya aiki ne da gwamnatinsa ta tsara kuma ta aiwatar a wani shiri na tabbatar da ilimin bai ɗaya ga dukkan yaran da suka isa zuwa makaranta a faɗin jihar.
“Tsarin ilimin Tsangaya ingantaccen tsarin ilimi ne a wannan yanki. Tsari ne da ake isar da tarbiyyar addini da kyawawan ɗabi’u ga duk wanda da ke cikinsa.
“Idan aka yi la’akari da muhimmancin tsarin ilimin Tsangaya ga al’ummarmu, za a ga cewa tsarin ya ƙunshi ilimin addinin Musulunci, wanda shi ne abin da Tsangaya ya mayar da hankali a kai, wanda kuma zai tafi daidai da ilimin zamani. Wannan yana nufin baiwa yaranmu ilimi da ƙwarewa don taimaka musu sanin yadda tsarin duniya ke tafiya a zamanance. Haɗa duka tsarin biyu, ita ce hanya mafi inganci ta kawo ƙarin ci gaba ga jama’armu da al’ummominmu.
“Saboda haka tsarin zai haɗe karatun Islamiyya da ilimin zamani. Gwamnati kuma ta shigar da shi cikin Shirin Ilimi Na Kowa a jihar.
“Za a koyar da darussa kamar Ingilishi, Lissafi, Ilimin zamantakewa, da koyar da sana’o’i tare da ilimin addinin Islama, tare da haɓaka ƙwarewar yara da jin daɗin rayuwa.
“Wannan aikin ya ƙunshi gina ɗakunan kwanan ɗalibai guda tara, gidajen kwanan malamai, katangar za ta kewaye makaratar, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru da tebura, wuraren koyarwa da koyo da dai sauransu.
“Bugu da ƙari, makarantar tana da cibiyar koyar da sana’o’i inda za a ba da horo a kan aikin kafinta, aikin katako, ɗinki, koyon aiki da kwamfuta da dai sauran su. Hakan zai ba su damar yin amfani da dabarun da suka samu tare da taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai.”
A Nasarawa Burkullu, ƙaramar hukumar Bukkuyum, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da babban asibitin da aka inganta daga cibiyar kula da lafiya ta matakin farko.
“Sabuwar ginin da aka inganta za ta samar da cikakkiyar aiki na kiwon lafiya kamar kulawar gaggawa, tiyata, kula da lafiyar mata da yara.
“Ayyukan da aka aiwatar sun haɗa da gina ƙarin gine-gine da kuma gyara waɗanda ake da su, kamar sashen keɓe masu lalura ta daman, wurin ajiyar gawa, sashen kula haɗari, ɗakin tiyata, ɗakunan tiyatar maza da mata, GOPD, ɗakin gwaje-gwaje, sashen magani, kula da mata masu juna biyu, da sashen kula da yara. Sauran sun haɗa da ɓangaren masu kula da asibiti, wuraren ma’aikata, masallatai, da rijiyoyin burtsatse.
A Ƙaramar Hukumar Maru, Gwamna Lawal ya tantance aikin gyaran babban asibitin Maru, wanda ya haɗa da gyaran dukkan gine-gine da samar da kayan aiki na zamani don bunƙasa ƙarfinta na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.