• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara Ɗaya Ta Mulkin Tinubu: Nijeriya Ta Fara Ganin Sauyi Wajen Samun Kwanciyar Hankali Da Arziki Da Tsaro – Minista

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
Shekara Ɗaya Ta Mulkin Tinubu: Nijeriya Ta Fara Ganin Sauyi Wajen Samun Kwanciyar Hankali Da Arziki Da Tsaro – Minista
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Nijeriya ta fara tafiya mai kawo sauyi ta fuskar samun kwanciyar hankali da arziki da tsaro, wanda Ajandar Sabunta Fata Mai Lamba 8 ta ƙunsa a cikin shekara ta farko tun bayan hawan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Ministan ya bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ma’aikatar sa ta fitar a ranar Talata mai taken “Shekara Ɗaya ta Gwamnatin Tinubu – Gina Nijeriya mai Tsaro, Ƙarfi, da Wadata,” wanda ke bayyana gagarumin cigaban da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, na tunkarar manyan matsalolin ƙasa da aiwatar da ingantattun manufofi da nufin samar da haɓaka da cigaban ƙasa.

  • Ina Kokarin Cika Alkawuran Da Na Dauka – Tinubu 
  •  ‘Yancin Taiwan Na Nufin Yaki, In Ji Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin

Rahoton ya ce, “A yayin da ake fama da matsalolin tattalin arziki da tashe-tashen hankula da rashin aikin yi suka haifar, sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta yi sun daidaita tattalin arzikin ƙasar tare da haifar da cigaba.

“Wani muhimmin yunƙuri shi ne kawar da tallafin man fetur maras ɗorewa, da karkatar da kusan dala biliyan 10 kowace shekara zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro.

“Wannan mataki kaɗai ya haifar da raguwar shigo da mai da kashi 50 cikin 100 tare da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na jihohi da ƙananan hukumomi. Kawar da tallafin kuɗin ƙasashen waje da kuma daidaita farashin canji ya ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan ya sanya Kasuwar Hada-hadar Hannun Jari ta Nijeriya ta zama kan gaba a kasuwannin duniya tare da ƙarfafa darajar Naira.”

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

Rahoton ya ƙara da cewa, “Domin samun sauƙin tasirin waɗannan matakan tattalin arziki, gwamnatin ta ƙaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da biyan albashin naira 35,000 ga ma’aikatan gwamnati duk wata, kafa kwamitin sake fasalin albashi, da kuma samar da Asusun Tallafa wa Jihohi.

“Ɓangaren ƙasa da ƙasa, gwamnatin ta samu nasarar jawo jarin sama da dala biliyan 30, wanda hakan ya ƙara haɓaka tattalin arzikin Nijeriya.

“Tsaro ya kasance babban abin da aka fi mayar da hankali a kan shi, tare da zuba jari mai yawa da nufin zamanintar da rundunonin sojoji da kuma cimma muhimman nasarori a harkar tsaron ƙasa.

“Wannan yunƙurin ya haifar da ‘yantar da mutane sama da 4,600 da aka yi garkuwa da su, tare da kawar da masu laifi 9,300, tare da kama ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 7,000.

“Jami’an tsaron sun kuma ƙwato dubban makamai da harsasai, wanda hakan na da muhimmanci wajen yaƙar ‘yan fashi da masu tayar da ƙayar baya.

A yayin da yake tunkarar matsalar samar da abinci, Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci, wanda ya kai ga sake fasalin Ma’aikatar Noma zuwa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci.

An ƙaddamar da shirye-shirye irin su Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa da Shirin Noman Rani don bunƙasa aikin noma da tabbatar da wadatar abinci.

“An inganta matakan tsaro wajen kula da makamashi da albarkatun ƙasa a yankin Neja Delta, lamarin da ya haifar da ƙaruwar haƙo mai da ƙarin iskar gas. Haka kuma an ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, tare da zuba jari mai yawa a hanyoyin sufuri da suka haɗa da ƙaddamar da sabbin layukan dogo da ƙaddamar da babban titin Legas zuwa Kalaba, da ƙaddamar da Tsarin Babbar Hanyar Sokoto zuwa Badagry.

“An haɓaka fannin kiwon lafiya da ilimi sosai a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata. Faɗaɗa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da gabatar da dokar ba da lamuni ga ɗalibai (Samun Ilimi Mai Girma) wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta hanyoyin samun muhimman ayyuka da damarmaki ga dukkan ‘yan Nijeriya.

“A yayin da muke ci gaba da tafiya, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta na tabbatar da Nijeriya mai ɗorewa da wadatar arziki, wadda za ta kasance ƙarƙashin zuba jari, da ƙarfafa matasa, da inganta harkokin mulki.

“Cigaban da aka samu a cikin shekara guda kacal ya kafa ginshiƙin haɓaka da cigaba mai ɗorewa, tare da yin alƙawarin samun kyakkyawar rayuwa a nan gaba ga dukkan ‘yan Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yan NijeriyaGwamnatin TinubuMinistan Yaɗa Labarai
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hakkin Bil Adam Iri Na Amurka Matakin Gatanci Da Babakere Ne

Next Post

Xi Jinping: Sin Na Fatan Kafa Tsare-Tsaren Hadin Kai Biyar Tsakaninta Da Kasashen Larabawa

Related

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas
Manyan Labarai

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

40 minutes ago
Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa
Labarai

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

3 hours ago
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Ra'ayi Riga

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

3 hours ago
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya
Rahotonni

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

6 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

15 hours ago
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Da Kubutar Da Mutum 16 Da Aka Sace A Kaduna
Labarai

ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000

16 hours ago
Next Post
Xi Jinping: Sin Na Fatan Kafa Tsare-Tsaren Hadin Kai Biyar Tsakaninta Da Kasashen Larabawa

Xi Jinping: Sin Na Fatan Kafa Tsare-Tsaren Hadin Kai Biyar Tsakaninta Da Kasashen Larabawa

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

‘Yan Kasuwa Na Neman Diyya Bayan Rushe Kasuwar Alaba Rago A Legas

August 26, 2025
Ɗaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

Ɗaruruwan ‘Yan APC Sun Koma ADC A Sakkwato Saboda Rashin Tsaro Da Talauci

August 26, 2025
Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa

ASUU Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Rashin Cika Mata Alƙawura

August 26, 2025
Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 26, 2025
Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

August 26, 2025
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

August 26, 2025
An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

August 25, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

August 25, 2025
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

August 25, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

August 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.