Shekara 10 kenan da sace ‘yan mata 276 na makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, an fitar da wani sabon rahoto da ke nuna cewa ‘yan mata 21 daga cikin wadanda aka sako ya zuwa yanzu sun dawo gida tare da yara 34.
Wannan yana cikin rahoton da Gidauniyar Murtala Muhammed (MMF) ta fitar ta kuma ta raba wa manema labarai a karshen mako a Abuja.
- Bangaren Amurka Ya Mayar Wa Bangaren Sin Da Kayayyakin Tarihi 38 Da Suka Bata Daga Sin
- Shari’ar Zargin Karkatar Da Dukiyar Al’umma: Ganduje Da Iyalansa Ba Su Halarci Kotu Ba
Kamar yadda gidauniyar ta ce, rahoton an yi shi ne domin tunawa da cika shakara 10 da sace ‘yan matan. Rahoton ya kuma tabbatar da cin zarafi da auren dole da ‘yan matan suka fuskanta a lokacin da suke tsare a hannun ‘yan ta’addan.
Haka kuma rahoton na gidauniyar ya kara bayyana cewa iyayen daliban aka sace su 48 ne suka mutu. Sauran iyayen daliban da ke raye kuma na rayuwa cikin tashin hankali da fargabar rashin sanin halin da ‘ya’yansu ke ciki.
Babban Daraktan gidauniyar MMF, Dakta Aisha Muhammad-Oyebode wacce ta gabatar da rahoton ta bayyana cewa, gidauniyar ta lissafa wasu muhimman shawarwari guda 10.
Gidauniyar ta ce ya kamata gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da kasashen duniya su ba da fifiko a kan wadannan shawarwari. Shawarwarin sun hada da, daukar ingantattun matakan tsaro, shirye-shiryen tallafa wa kuyuka da tsarin ankararwa cikin gaggawa dangane da barazanar tsaro.
Ta ce, “A cikin shekara 10 tun lokacin da aka yi garkuwa da ‘yan matan Chibok ya janyo fusata al’ummar duniya gaba daya, kowani al’amari ya sauya a Nijeriya, inda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da cin karansu babu babbaka na tsawon shekaru masu yawa.
“A daidai lokacin da Nijeriya ke fama da annoban garkuwa da mutane wanda ba ta nuna alaman raguwa ba, muna kira ga hukumomin Nijeriya da na kasa da kasa su dauki muhimman matakai domin magance abubuwan da ke janyo rikice-rikice da tashin hankali kan mata, wadanda suka hada da fatara, rashin natsuwa da tabarbarewar tattalin arziki.
“Rahoton ya gano cewa cikin 91 na daliban makarantar guda 276 har yanzu ba su san inda aka dosa ba.
“Rahoton ya kuma bayyana cewa ‘yan matan Chibok 21 da aka sako sun samu sun dawo da yara 34, wanda ya nuna sun fuskanci cin zarafi na jin jima’I da su da kuma tilasta musu yin auren dole lokacin da suke tsare.
“Rahoton MMF ya bayar da shawarar cewa a yi kokarin magance tushen yin garkuwa da mutane, sannan ya bukaci karfafa hadin gwiwa na kasa da kasa wajen daukar matakan kawo karshen lamarin.”
Ta kuma bayar da shawarar a dauki matakin tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu kan wannan mummunan labari komin matsayin da suke da shi doka ta yi aiki a kan kowa.