Haruna Uba" />

Shekara 70 Da Mamayar Palasdinu

Palasdinu kasa ce mai dogon tarihi, sannan kasa ce mai tasiri ga al’ummar musulmi na duniya. Kodayake ma har da al’ummar Kirista wannan kasa tana da muhimmancin gaske a wurinsu. Annabawan Allah da dama sun yi zamani a wannan kasa wasu daga cikinsu ma kaburburan su na cikin kasar. Kafin halin da al’ummar Palasdinu su fada cikin halin da suke ciki yau na mamayar Yahudawan Sahayoniya, da ma dai ita kasar ta kasance karkashin dauloli daban-dabam. Zamani bayan zamani. Idan abin a takaita ne,Daular Usmaniyya, mai hedikwata a Istanbul din da take kasar Turkiyya ita ce uwargijiyar kasar Palasdinu ta karshe.

Daular ta Usmaniyya ta yi tashe ainun a zamanin da take tsaka da mulkinta wadda ta ja zarenta tsakanin shekarun 1517 zuwa 1917 na miladiyya. A lokacin da Daular Usmaniyya take shimfida mulkinta,kasahen da yanzu ake kira da Labanon, da Siriya da ita kanta Palasdinun da muke magana akanta duk suna karkashin daular. Ba ma kawai wadannan kasashe ba har ma da kasashe irin su Romania, da Sabiya, da Bosniya, da Albaniya, da Montenegro, da Bulgaria da kuma irin su Cyprus da dai sauransu duk suna tsohuwar Daular ta Usmaniyya. Yakin duniya na farko daya afku tsakanin 1914 zuwa 1918 ana danganta shi daga cikin manyan abubuwan da su ka kawo karshen daular saboda ita Turkiyyan ta bai wa Jamus goyon baya. Saboda haka bayan rusa cin Jamus a wannan bakin sai turawan mulkin mallakar su ka yiwa Daular ayaga. Kasashe Birtaniya da Faransa su ka rarraba kasashen da suke karkashin daular a karkashin mulkin mallakarsu. Kasashe irin su Lebanon da Siriya Faransa ta mallakesu sai Palasdinu da Jordan da Gabar Yamma (West Bank) Birtaniya ta mallakesu. A wannnan lokaci sam ba a zancen Israila balle wasu wai Yahudawan Sahayoniya, ko da yake dai akwai Yahudawan amma fa sam ba a zancen wata kasa wai ita Israila.

 

Yan mulkin mallakar da suka mamayi wadannan kasashe su ka raba su tsakaninsu,sun fake da wata yarjejeniya da suke kira ta da suna “Skye’s Picot Agreement” da aka yi a shekarar 1916. Ingila ba abin da ya sha mata kai a waccan zamanin illa ta yi mulkin mallaka, ta mamayi kasa,sannan ta dinga tatsar arzikin wannan kasar. Sai dai a lokacin da ita Ingilar ta shagaltu da yawon mulkin mallaka,Yahudawa sun sami damar kutsawa cikin kasar ta Ingila domin hako zinare da sarrafa shi tun da lokacin akwai zinare makil a Ingilan kuma shi ne tattalin arzikin duniya a lokacin. Haba wa! Ita Ingila na yawon sarauta da mallaka kan ta farga ai duk arzikin kasarta ya koma hannun Yahudawa. Wannan ya sa Yahudawa su ka salladu akan Ingila, su ke kada ta duk inda suke so.

Ana cikin wannan hali na Yahudawa sun zame wa Ingila karfen kafa. Sai su Yahudawan su ka sake fahimtar cewa lallai Amurka ta na dan tasowa a lokacin,duk da cewa ita Amurka ba ruwanta da yi wa wata kasa mulkin mallaka,bil hasali ma ita Amurkan Birtaniya ce ta yi mata mulkin mallakar. Dagowar Amurka shi ya kara karfafa tunanin su Yahudawan shiga ita ita ma su mai da ta hannunsu kamar yadda Ingila take a tafin hannunsu. To amma da wacce hanya za su fake su fada Amurka? Fatansu shine gina Amurka da bunkasa ta a duniya da mai da ta kakkarfar kasar da za ta ke basu kariya, tun da su basu da wata tasu ta kan su.

Akwai wata wasika da Sakataren Mai kula da kasashen da Birtaniya take yi wa mulkin mallaka mai suna Sir Arthur Balfour wanda ya aikawa shugaban Yahudawa mazauna Ingila ana kiransa da Lionel Walter Rothschild a shekarar 1917. Wannan wasika ta shahara da suna “Balfour’s Declarations of 1917” wato (Shelar Balfo ta 1917). A cikin wasikar Balfour ya jaddada wajibcin Ingila ta samarwa Yahudawa kasa ta su ta kashin kan su. Kuma tun a lokacin ya yi ishara da cewa Palasdinun da a lokacin ta na karkashin mulkin mallakar Ingila ita za a mallakawa Yahudawa.

Amsar yadda Yahudawa su ka bi wajen kutsawa Amurka da mallakar ta shine; sun shugabanci wasu mutane daga Turai, aka tura can Amurka. Abin da ake so su yi shi ne ,kashe shugabanni asalin Amurkawan da ake kira da Indiyawan daji (red Indians) wadanda da su wadannan Indiyawan dajin su ne makil a Amurka. Amma yanzu duk sun kaura, har ma yanzu ya zama muzantawa ka kira Ba Amirke da wannan sunan. Saboda haka, shugabannin Turawa suna aikawa da Indiyawan daji lahira, su kuma Yahudawa a daya bamgaren su na ta diban zinariyar Amurkawan da ake karkashewa kafin ka ce kwabo ai kusan duk arzikin Amurka ya koma hannunsu,da wannan dukiyar su ka kafa manyan kamfanoni,da dukiyar su ka kafa cibiyoyin hada-hadar kasuwanci na duniya,da dukiyar su ka mallaki makamai da kamfanonin kera su abubuwan da ya ba su cikakkiyar damar juya shugabannin Amurka kamar waina. Ba ka isa zama shugaba ba sai da amincewarsu su ka kafa kungiya mai karfi da har yau ba bu wanda ya isa zama shugaban Amurka sai da yardarsu.

Ana cikin yanayin hanyoyin da za a samarwa Yahudawa muhalli, kwatsam sai yakin duniya na biyu ya barke.Hitler ya tasamma kasashen Turai ya kuma gigita su da yaki. Babu shakka wannan yanayinne ya baiwa Yahudawa damar fuskantar shugabannin Turai, su ka ce ‘to kun ga fa Hitla tsiyar da yake yi,gaba daya ya kame kasashenku na Turai, Ingila da Norway ne kadai su ka rage. Su ma din yana juyowa kan su zai gama da su. Ba za ku iya yaki da shi ba, yafi karfinku, amma idan kun yi mana alkawarin bayan bakin za ku taimaka mana mu ma mu kafa kasarmu ta Yahudawa to kuwa mu na da karfi na makamai a Amurka da zamu taimake da shi. Za mu shigo da Amurka cikin yakin ta taimaka mu ku”

To amma, da wanne irin dalili za a gamsar da duniya idan aka ga rana tsaka Amurka da tsunduma cikin yakin da baruwanta ba kuma da ita ake yi ba? Saboda har wajen shekarar 1940 da wani abu Amurka sam ba ta cikin wannan yaki. To da ma akwai kyakkyawar fahimta da danganta mai kyau tsakanin kasar Jamus da kuma kasar Japan. Sannan ita Japan din ta na da wasu tsibirai a kogin Pacific, Amurka kuma ta na da nata tsibiran a can jihar Hawaii mai makobtaka da Japan. A Palhaba akwai jiragen ruwa na Amurka sai Yahudawan su ka kulla makircin cewa za su sa Amurka ta ba da rahoton karya su aika Japan cewa sun samu rahoton ita Japan din za ta kawo wa Amurka hari. Saboda haka Japan ba ta masaniyar ramin da aka haka ma ta, lokacin da ta kama wadannan jirage na Amurka sai duk ta nutsar da a ruwan Amurka na Palhaba. Nan da nan Amurka ta fake da wannan harin ta shigo yakin, ai kafin wani lokaci har dagargaza Jamus.

Sannan kammala yakin ke da wuya a shekarar 1945 sai Ingila ta fara yunkurin biya wa kuturu ladan aski. Domin kuwa ranar 29 ga Nuwambar 1947,Ingila ta aika da takarda zauren Majalisar Dinkin Duniya neman samar da kasashe biyu a Palasdinu wato Isra’ila da Palasdinu. Wanda ita kan ta MDD din shekararta biyu kacal da kafa ta. Nan da nan kuwa zauren majalisar ya kada kuri’ar amincewa da wannan bukata ta Ingila. A shekarar 1948 yau shekaru saba’in cur kenan aka tabbatar da sansanin ‘yan ta’adda, mabarnata masu kashe mata da jaririai a matsayin kasar Isara’ila. Haramtacciyar a cikin kasar Palasdinu wadanda a tsawon shekarun nan ba bu abin da suke sai ta’addancin kashe-kashe da rushe-rushen gidaje. Kuma abin mamaki kullum kara fadin kasar ta Israilan suke domin wadannan ‘yan share wuri zauna sun nunnunka iya shacin wurinma da aka shata mu su,kuma har yanzu ba su daina mamayar ba!

Sai dai da ma can su Yahudawan Sahoyoniya basu boye mummunan shirinsu na fadada Isra’ilan ba. David Ben-Gurion Firayim Ministan Isra’ila na farko ya taba cewa “za mu iya karbar wurin da aka shata mana yanzu, ba kuma wata kasa da za ta ce mu tsaya iya wannan iyakar da aka shata, iyakokin Isra’ila al’amari ne na Yahudawa”. Shi ma Menachem Wolfovitch Begin wanda shine Firayim Ministan Isra’ila na shida daga mulki Isra’ilan faga 1977-1983 ya jaddada maganar Ben-Gurion a shekarar 1951 yace “ba zai yiwu ba, a yiwa Isra’ila iyaka ba…..”

Wannan shi ne a takaice yadda aka kafa Isra’ila da kuma ci gaba da mamayar kasar Palasdinu. Wanda a tarihin kasashen duniya babu wata al’umma da aka jefa su cikin kuncin rayuwa kamar Palasdinawa. Rana tsaka aka zo aka  kwace musu kasa ta hanyar yaudara da tsararren ta’addanci, da gidajensu amma an maida da su rayuwa a sansanonin gudun hijira. Duk da haka ba a barsu ba sai binsu ake ana farauyarsu, ana tozarta su. Wani abin tausayin su ake zalunta, amma kuma su ake zargi sannan makasansu su ne ‘yan lelen Turawa!

Wannan zura idon da duniya ta yiwa Palasdinawa da kuma halin-ko-in -kula da kuncin da su ke ciki yasa marigayi Imam Khumaini (KS) ya kira al’ummar duniya masu ruhin yan Adamtaka da su fito kwansu-da-kwarkwatarsu a irin wannan rana ta Juma’ar karshen Ramadan domin nu na goyon baya ga raunanan Palasdinu da kuma la’antar Yahudawan Sahayoniya da duk mai goya mu su baya. Babu shakka Allah ne ya kimsa wa Imam wannan hikima ta farkar da duniya halin da Palasdinawa su ke ciki ta hanyar jerin gwano. Amma koma menene sirrin a hakikanin gaskiya ana iya fahimtar tasirinsa musamman ta yadda su Yahudawan Sahoyoniya su ka fi nu na damuwarsu a fili a duk irin wannan rana ta jerin gwanon goyon bayan Palasdinu. Wannan na kara tabbatarwa da duniya cewa ko shakka babu wannan haramtaciyyar kasa ta Isra’ila ba mai tabbata ba ce. Har ma a cikin maganganunsa na hikima Imam (KS)  yake fadin cewa “da duk musulmin duniya za su kawo gudummawar bokiti na ruwa a zuba a Isra’ila to da an hallaka Yahudawa Sahayoniya”

 

Exit mobile version