• English
  • Business News
Saturday, June 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara Biyun Mulki Tinubu: Nasarori Da Matsaloli Da Inda Aka Dosa

by Sani Anwar
3 weeks ago
in Manyan Labarai
0
Shekara Biyun Mulki Tinubu: Nasarori Da Matsaloli Da Inda Aka Dosa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A wannan mako da muke ciki ne, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara biyu cif kan karagar mulkin kasar nan.

Sakamakon haka ne yasa LEADERSHIP Hausa ta yi waiwaye, domin zakulo nasarori, matsaloli da kuma inda akalar gwamnatin ta dosa a halin yanzu, kama daga bangaren harkokin tattalin arziki, tsaro, lafiya, ilimi da sauran makamantansu.

A lokacin da aka rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Nijeriya na tattare da matsaloli da kalubale iri-iri, wanda ba ta taba fuskanta a tarihinta ba, musamman ta fuskar tabarbarewar tattalin arziki da kuma koma-bayan da aka samu ta fuskar kudaden shiga na man fetir da kudaden da ake handamewa na tallafin man.

Har ila yau, akwai kokarin ganin an sake daidaita kudaden kasashen wajen da ya jima yana ci wa kasar tuwo a kwarya da kuma batun matsalar hauhawar farashin kayayyakin da ya addabi dukkanin al’ummar kasar.

  • Tinubu Ya Yi Ƙoƙari, Gyaran Nijeriya Aikin Kowa Da Kowa Ne – Buhari
  • Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu, Ya Yi Gargaɗi Kan Cin Sabon Bashi

Sakamakon wadannan matsaloli da gwamnatin ta Tinubu ta gada, gwamnatin ta bayyana yadda ta yi amfani da kafofin sadarwa, jajircewa da kuma kwatanta gaskiya ta hanyar fitar da sabbin tsare-tsaren da za su ciyar da kasar gaba, kamar yadda yake a cikin shirin da aka yi wa lakabi da ‘Renewed Hope Action Plan’.

Labarai Masu Nasaba

Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa

A wannan zango na shekaru biyun Tinubu, ma’aikatar yada labarai ta kasa; ita ce ginshikin aiwatar da wadannan dabaru da tsare-tsare, musamman ta fuskar sake fasalin hukumomi, aikewa da sakwannin jan kunne da ladabtarwa da kuma jin ra’ayoyin daidaikun mutane, wanda hakan ya bai wa gwamnatin damar sanin matsalolin ‘yan kasa da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su.

Tunda farko, ma’aikatar karkashin jagorancin ministanta, Alhaji Mohammed Idris, ta yi kokarin aiwatar da aikin da ta sanya gaba; ta hanyar nuna babu sani babu sabo ga ma’aikatun gwamnatin da suka keta doka da oda baki-daya, domin kuwa haka ma’aikatar ta kasa zaune, ta kasa tsaye wajen bibiyar ‘yan Nijeriya a wureran ayyuka da sauran wuraren zamansu, don jin irin halin da suke ciki.

Har wa yau, manufofin ma’aikatar sun bayyana a sarari, musamman ta fuskar inganta hadin kan kasa, ta hanyar bai wa ‘yan kasar dama da kuma aiki da kafafen yada labarai tare da kokarin tantance labarun gaskiya da kuma sauraron ra’ayoyin mutane daban-daban lokaci bayan lokaci ta hanyar yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, don tattara bayanai da kuma tattauna sauran al’amuran gwamnati.

Haka zalika, cire tallafin man fetir da gwamnatin ta yi tare da kawar da rabe-raben farashin dala, ya yi matukar girgiza kasar duk kuwa da cewa, an jima ana kokawa a kansu.

An gudanar da zama a dukkanin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya, inda aka samu bayanai da dama da ake bukata dangane da matakan da gwamnati ya kamata ta dayuka, wajen magance matsalolin al’umma; wanda ya hada da tsarin bai wa dalibai bashin karatu, shirin samar da motoci masu amfani da gas, domin samun saukin kudaden sufuri, kirkirar sabbin hanyoyin kasuwanci ta hanyar amfani da fasahar zamani, shirin bai wa kananan ‘yan kasuwa da masana’antu rance da sauran makamantansu.           

Bisa la’akari da rawar da take takawa wajen wayar da kan jama’a a kan ayyukan gwamnati, ma’aikatar yada labarai da wayar da kan al’umma ta kasa, ta yi fice wajen kwatanta yadda gwamnatin ke sake farfado da tattalin arzikinta.

A wannan shekara ta 2025 kadai, gwamnatin ta ware Naira tiriliyan 2.5 a aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Kalaba da kuma na Badagiri zuwa Sakkwato, wanda a tarihin aikin sheka-shekara, shi ne aiki na farko mafi girma, sannan ga batun farfado da matatun man fetir na Fatakwal da Warri da kuma sake gina madatsun ruwa na Alau da ke Jihar Borno.  

Kazalika, sabbin ma’aikatun ci gaban yankuna da kiwo, a shirye suke wajen habaka ayyukan gona, kazalika shirin nan na shugaban kasa na samar da motocin sufuri masu amfani da iskar gas, ya samar da sama da dala miliyan 450, domin samar da ingantattun kayayyakin aikin man fetir.

Haka nan, hukumar kula da bayar da lamuni ta dalibai (NELFUND), ta bayar da tallafin karatu ga dalibai kimanin 300,000; wanda hakan ya bude kofar damar bayar da bashi, don sayen gidaje da harkar kiwon lafiya da kuma kananan kasuwanci, sannan akwai Naira biliyan 200 da aka ware wa masu kasuwancin nano, inda hakan zai taimaka wa matsakaita da kananan masana’antu wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Wadannan ba kididdiga ba ne kadai, miliyoyin ‘yan Nijeriya sun amfana da su, suna kuma ci gaba da amfanarsu, kamar yadda gwamnatin ke ikrari.

Akwai kuma batun ribanya kudaden shiga da wannan gwamnati ta yi, domin kuwa kamar yadda gwamnatin ta bayyana; jimillar kudaden shiga na gwamnati sun ninka fiye da sau biyu, wanda ya kai kimanin tiriliyan 1.9, tun a farkon shekarar 2024; idan aka kwatanta da shekarar 2023, sakamakon toshe wasu hanyoyi da kudaden ke zurarewa.

Har ila yau, gwamnatin ta bayyana yadda ta rage kudaden da ake kashewa tare da biyan basussuka daga kashi 97 zuwa kashi 68 cikin 100 a cikin watanni 13 kacal tare da biyan basussukan waje na kimanin dala biliyan 5, ba tare da kawo wani cikas kan shirye-shiryen da suka sanya a gaba ba.

Duk dai a cikin nasarrorin da gwamnatin ta bayyana ta samu, akwai batun zuba hannun jari kai tsaye daga kasashen waje, wanda a cewarta; masu zuba hannun jarin yanzu suna dawowa, domin kuwa akwai wasu kamfanonin guda biyu da suka rattaba hannu a kan sama da dala biliyan daya, tun bayan bijiro da sabbin tsare-tsaren nata.

A bangaren habaka masana’antu kuwa, gwamnatin ta bayyana yadda ta bayar da rancen Naira Biliyan daya-daya ga daidaikun masu manyan masana’antu domin kara habaka su, sannan kuma ga batun mafi karancin albashi na kasa, “Na sanya hannu kan mafi karancin albashin ma’aikata tare da tabbatar da cewa; ma’aikatan mafi karancin albashin da za su rika samu, ba zai gaza akalla Naira 70,000 a kowane wata”, in ji Tinubu.    

Haka nan, a bangaren ayyukan noma, Gwamnatin Tinubu ta samar da tallafi na musamman ga manoma, domin samun damar noma abinci mai yawa da kuma karyewar farashinsa.

Duk dai a cikin shekaru biyun Tinubun, gwamnatin ta janye haraji ga wasu daga cikin kayayyakin da suka hada da Shinkafa, Alkama, Masara, Magunguna da sauran wasu daga cikin kayayyakin da suka shafi fannin kiwon lafiya na tsawon watanni shida, domin karya farashinsu.

Sannan, akwai batun raba Takin Zamani ga manoma, don cimma burin gwamnatin na ganin an bunkasa abincin da ake nomawa a cikin gida, ta hanyar noma akalla hekta miliyan 10, wanda gwamnatin tarayya ta bayar da dukkanin tallafin da ake bukata, inda jihohi su kuma suka samar da wadannan gonaki ga manoman.

Kazalika, gwamnatin tarayyar ta samar da kayayyakin noma na zamani, wadanda suka hada da Tarakta da sauran kayayyin aikin noma na biliyoyin Nairori daga Kasar Amurka da Belarus da kuma Brazil.

Bugu da kari, gwamnatin tarayya ta bai wa Jihohi Nijeriya 36 tallafi na sama da Naira biliyan 570, domin kara fadada hanyoyin tallafa wa ‘yan kasa. Kana a bangaren kokarinta na ci gaba da bunkasa harkokin kasuwanci, ta kudiri aniyar bai wa akalla masu kananun sana’o’i kimanin 75,000 bashin Naira miliyan daya-daya.

Akwai kuma batun yadda za a habaka tattalin arzikin kasa ta hanyar shirin nan na samar da muhalli. Gwamnatin Shugaba Tinubu, ta kudiri aniyar samar da dubban ayyukan yi ta hanyar gina gidaje akalla 100,000, cikin shekaru uku kacal.

A bangaren kalubale kuwa, manyan al’amura guda biyu su ne suka fi ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya, wato batun matsalar tsaro da kuma tattalin arziki.

Idan aka dubi matsalar fannin tsaro, musamman a Arewacin wannan kasa, za a iya cewa; kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, domin kuwa har zuwa yanzu; ana ci gaba da yin garkuwa da mutane tare da neman kudaden fansa a Jihohin Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kaduna da sauransu.

Kazalika, ‘yan ta’adda na ci gaba da tashin garuruwa da dama daga cikin wadannan jihohi na Arewacin Nijeriya, ta hanyar kone garuruwan ko far musu a kowane irin lokaci.

Koda-yake, batun garkuwa da mutanen bai tsaya kadai a Arewacin kasar ba, har ma da wasu daga cikin jihohin kudancin kasar su ma na fama da ire-iren wadannan matsaloli.

Sannan, uba-uba ga batun matsalar ‘yan kungiyar Boko Haram, wanda a halin yanzu za a iya cewa; sun sake dawowa da karfinsu. Duk da cewa; sojojin Nijeriya na iya kokarinsu a kan ‘yan kungiayar, amma su ma suna yi musu barna ta hanyar hallaka wasu daga cikinsu tare kuma da kwashe musu makaman yaki kamar yadda al’amarin ya faru kwanan nan.

Haka nan, batun matsalar tattalin arziki, har yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar Naira.

Sai kuma batun inda aka dosa a halin yanzu, wanda batu na gaskiya shi ne, za a iya cewa; kusan hankalin gwamnati ya fi karkata a kan sha’anin harkokin siyasa ko kuma zaben da ake tunkari na 2027, tare da tunanin yadda za a samu nasarar cin zaben.

Duk da cewa, ayyukan gwamnati ba za su taba tsayawa ba, musamman a bangaren al’amuran ta’addanci da ya addabi kasar, amma babban al’amarin da ya fi tayarwa ‘yan siyasa hankali a halin yanzu shi ne, yadda za su tunkari zaben da kuma yadda za su lashe shi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Atiku da TinubuShettima
ShareTweetSendShare
Previous Post

Cutar Hawan Jini Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke

Next Post

Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya

Related

Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 
Manyan Labarai

Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 

1 hour ago
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)
Manyan Labarai

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa

3 hours ago
Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista
Manyan Labarai

Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista

14 hours ago
Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto
Manyan Labarai

Ba Tsoro Ne Yasa Muka Amince Da Sulhu Da Ƴan Bindiga Ba – Gwamnatin Sokoto

19 hours ago
Tinubu Zai Zaɓi Mataimakinsa Bayan Taron Jam’iyya – Fadar Shugaban Ƙasa 
Manyan Labarai

Tinubu Zai Zaɓi Mataimakinsa Bayan Taron Jam’iyya – Fadar Shugaban Ƙasa 

22 hours ago
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Filato, Mutane 15 Sun Mutu A Bokkos Da Mangu
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Filato, Mutane 15 Sun Mutu A Bokkos Da Mangu

23 hours ago
Next Post
Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya

Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata

Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata

June 21, 2025
Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 

Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi 

June 21, 2025
Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje

Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje

June 21, 2025
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa

June 21, 2025
Rundunar PLA Ta Soki Birtaniya Bisa Zuzuta Abun Da Ya Wakana Yayin Da Jirgin Ruwan Sintirinta Ya Keta Ta Zirin Taiwan 

Rundunar PLA Ta Soki Birtaniya Bisa Zuzuta Abun Da Ya Wakana Yayin Da Jirgin Ruwan Sintirinta Ya Keta Ta Zirin Taiwan 

June 20, 2025
Hadin Gwiwa Da Sin Na Bunkasa Zaman Lafiya Da Daidaito A Yankin Kahon Afirka

Hadin Gwiwa Da Sin Na Bunkasa Zaman Lafiya Da Daidaito A Yankin Kahon Afirka

June 20, 2025
Me Ya Kamata Mai Yaron Ciki Ta Kula Da Shi?

Me Ya Kamata Mai Yaron Ciki Ta Kula Da Shi?

June 20, 2025
Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista

Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista

June 20, 2025
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

June 20, 2025
Sin Ta Jadadda Wajibcin Daukar Jerin Matakan Magance Matsalar Talauci Da Karancin Ci Gaba Da Rikici

Sin Ta Jadadda Wajibcin Daukar Jerin Matakan Magance Matsalar Talauci Da Karancin Ci Gaba Da Rikici

June 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.