ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya

by Khalid Idris Doya
1 year ago
Tallafi

Shekaru biyu bayan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki matsaya a watan Mayun 2023 na dakatar da biyan tallafin man Fetur, gwamnatin tarayya ta samu damar tara rarar zunzurutun kudade har naira tiriliyan bakwai, amma tsananin rayuwa da yunwa na ci gaba da addabar ‘yan Nijeriya da kuma kananan kasuwanci. 

Kananan sana’o’i wadanda tun da can suna ta faman fadi-tashi ta yadda za su ci gaba da gudanuwar da harkokinsu, maimakon sauyi sai kara koma-baya ake samu, lamarin da ya tilasta wa wasu da dama rufe harkokin sana’o’in nasu, don haka an kara samun marasa ayyukan yi a cikin kasar nan.  

  • Darajar Sashen Masana’antun AI Na Sin Ta Kai Kusan Yuan Biliyan 600
  • Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja

Masu ruwa da tsaki dai sun yi gargadin cewa ci gaba da samun tsadar kudin sufuri da na kudaden sarrafa kayayyaki su ne ke janyo tashin kudaden kayan bukatun yau da kullum, inda kuma gwamanti ce ke da alhakin dinke bakin zaren na tashin farashin kayayyakin masarufi.

ADVERTISEMENT

Masu nazarin lamura sun yi kira da a farfado da lamarin tara kudaden shiga na jihohi, ciki har da neman zamanantar da tsarin tattara kudaden haraji, sanya dabaru wajen kyautata kudin shiga, tabbatar da ana biyan kudaden domin karfafa yanayin kudin jihohi da kuma tabbatar da cewa kudaden da jihohi ke amsa daga asusun hadaka na gwamantin tarayya ana amfani da su yadda ya dace. 

Duk da kashe dala biliyan 2.9 wajen gyaran matatun man, kamfanin kula da albarkatun man fetur na kasa (NNPC) ya gaza farfado da matatun man gwamnati, abin da ya sa kasar har yanzu ta dogara da shigo da man fetur sama da kashi 60 cikin 100 daga kasashen waje da take sha a kullum.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Wani masanin tattalin arziki, Ademola Adigun, ya ce, duk da janye tallafin mai, sashin mai a Nijeriya ba ya tafiya kan ka’ida.

Ya yi bayanin cewa kawai an rage biyan tallafin ne amma ba wai an daina biya gaba daya ba, kuma babu gasa tsakanin ‘yan kasuwa wanda shi ma na haifar da nakasu. 

Adigun ya soki tsarin sayar da danyen mai a kan kudin naira domin zabar da masu saye, ta yadda za a samar da lamari kamar na ‘ya’yan mowa da bora, da ke iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, lamarin da ya tilasta wa kusan gidajen mai 5,000 rufewa.     

Adigun, duk da ya nuna farin ciki kan yadda masu zuba hannun jari suke nuna sha’awar zuba jari a sashin gas da yaba wa kan farfado da yanayin kasafin kudi, sai dai ya yi gargadin cewa har yanzu kasuwannin Nijeriya ba su da karfin janyo hankalin dandazon masu zuba jari.

Don haka ne ya yi kira da a samar da sauyi kan hanyoyin sufuri domin rage kudaden kayayyaki, ya ce, yawan kudin sufuri ne shi ne babban dalilin da ke janyo tashin farashin kayayyakin masarufi a kasar nan.

Shugaban PETROAN, Dakta Billy Gillis-Harry, ya ce, gwamnati ta kasa fito da abubuwan da ake sa rai ko ake tsammani da kuma cikakken tsari kan cire tallafin mai. 

Ya koka kan matsalolin da har yanzu ake ci gaba da samu kan sauran matatun mai na gwamnatin tarayya.

Tallafi
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (2)

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (2)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.