HALIMA UBA JALIL daya ce daga cikin fitattun mata ‘yan siyasa a Jihar Kano. A tattaunawarta da BUSHIRA A. NAKURA ta yi nitso a cikin kogin siyasar Kanawa da yadda wasu mata ke bata musu suna a fagen siyasa da sauran al’amura da suka shafi shugabanci a jihar. Ga cikakkiyar tattaunawar kamar haka:
Da farko masu karatu za su so sanin cikakken sunanki da tarihin ki a takaice…
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta
- Wani Alhaji Ya Sake Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta A Makkah
Amin wa’alaikum salam warahamatullah wabarakatuhu. Sunana Halima Uba Jalli, ni ‘yar kasuwa ce kuma ‘yar siyasa, an haife ni a Kano na yi makarantar Firamare a Festibal daga nan na ci gaba da ba karatun allo muhimmanci, sanin kowa ne a da iyayenmu ba su ba (karatun) Boko muhimmanci ba musamman ma karatun ‘ya mace ga shi na fito,a babban gida kuma gidan Malamai, wannan ya sa karatuna na Boko ya tawaya amma Alhamdulillahi tun da na samu karatun da zan bautawa Allah kuma da shi ne na samu ilimin zaman duniya ta yadda nake zaune da kowa lafiya yara da manya ko a hakan ma ce Alhamdulillahi. An yi min aure ina da ‘ya ‘ya shida; maza biyu mata hudu.
Shekararki nawa kina harkar siyasa?
To Alhamdulillah ni dai a yanzu ina ga akalla na kai shekara ashirin da biyar ko ma na zarce haka ina gwagwarmayar siyasa.
Me ya ja hankalinki da ya sa har kika fada harkokin siyasa Kuma ta yaya kika shiga ko kawai wayar gari ne kika yi kika gan ki cikin harkar?
Eh to, gaskiya akwai sanadi domin kin san komai na rayuwa yana da sanadi, sanadi mai kyau ko akasin haka, misali na auri matata ta sanadiyyar wance ko wane kuma muna zaune lafiya gaskiya na ji dadin wane ko wance sun yi min abu mai kyau, kin ga wannan sanadi ne mai kyau, ko na sayi wannan abin ne ta sanadiyyar wane ko wance kuma an cuce ni an siyar mani abu marar kyau gaskiya ban ji dadi ba da wane ya hada ni da wanda ya cuce ni, kin ga ai duk sanadi ne.
To a lokacin Musa Gwadabe akwai wasu Aminaina Hajiya Rabi da Hajiya ‘Yarja, to kusan a gidan nan suke rayuwarsu in za su fita harkokin siyasa sai in yi ta yi masu dariya a haka har ma Allah ya sa na zo na tsinci kaina a ciki, sai dai bana fita harkar kamfen (yakin neman zabe) amma duk wata gudummawa ina badawa amma in za a yi taro ina zuwa, ta hakane har lokacin da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya fito wata rana yazo a nan kofar Famfo ofishin ‘Yarja, ina ta (kiran) Babana, Babana, ni kuma Allah ya sa min kaunar Kwankwaso domin gaskiya komai zan iya yi saboda shi, kuma zan iya bayarwa Saboda shi da Allah ya sa ya fito kamfen sai na sake daura damara na shiga ake damawa da ni, zan yi da kudina zan yi kuma da jikina kuma daga nan mazaba ta Gwale saboda an ga irin gudunmawar da nake bayarwa ba na mantawa Marigayi Allah ya jikan sa da gafara Dakta.Hafizu Abubakar sai ya zamana kamar ma shi ne ubangidana, har Allah ya sa ma Ciyaman na Gwale Allah ya jikan rai Mairiga in za a yi wadansu abubuwan a nan gidan zai ce dan Allah a yi masu girki za a yi turo yau a turo su Abduhadi su zo su dauka a je a ci kyauta ni da ma ba wani abu nake karba ba haka nake yi musu har da su ruwa da lemo na ba su izinin duk wata gudunmawa da suke bukata in dai akan Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ne su zo zan bada koma mene ne.
To a haka dai ana cikin wannan cukurkudar har Allah ya kawo min miji na zo na yi aure mijina ya ce sam shi bai yarda da in ci gaba da fita harkokin siyasa ba sai dai in ci gaba da kasuwanci, a haka dai shekararmu goma sha biyu da shi a haka ya hana ni na hakura da kuma Allah ya kawo rabuwa aka rabu. Aurena yana mutuwa sai aka ce ga shi Dakta Rabiu Musa Kwankwaso zai sake fitowa takarar Gwamnan Jihar Kano na sake yin kundunbala da ma dai can ni ‘yar gwagwarmaya ce domin haka ko wane zama ne kawai bana halatta amma ban daina bada gudunmar da na saba ba, nakan sa ‘ya’yana idan za a fita kamfen ko wata gidauniya ta dalibai.
To a haka har Allah ya cika min burina Injiniya Abba Kabir Yusuf dan waliyyin Allah Balaraben gwamna ya haye wannan kujerar mulkin Kano mai albarka. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Yanzu kuma muna sa rai insha’Allahu 2027 Maigirma Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama Shugaban kasa da yardar Allah shi ne mafi alheri a gare mu.
To wannan kai daga ji kin san yarfe ne na siyasa kuma da ma ba za a rasa ‘yan adawa ba, Abba Kabir Yusuf wallahi gwamna ne mai adalci dan waliyin Allah mai hakuri mai karamci mai wasa da dariya, duk mutumin da bai rabu da shi ba, zai yi masa wannan sharrin, wallahi wallahi Injiniya Abba Kabir Yusuf mutumin kirki ne kuma kafin a samu irin Injiniya AbbaKabir Yusuf Gwamnanmu mai karamci bawan Allah dan sharifan Allah sa za a sha wahala.
Yanzu ina gaya miki a shekara takwas din da Ganduje ya yi shekara dayan Abba ta fi ma mutanen Kanon albarka, ba ma mutanen Kano ba makotan Kano ma suna fada muna da wannan labarin mun sani, kuma ga gari ya jiku rahamar Allah ta shigo an daina sace-sace an daina fizgar waya da duk wasu abubuwa, yanzu hankalin kuwa kwance yake kowa ya dawo mutum ga tallafawa mata. Kwanan baya ya tallafawa mata mutum dubu daya da dari biyar, da naira dubu hamsin-hamsin ga na maza da aka raba musu kayan zuwa mazabu-mazabu, da ana fargabar za a yi yunwa za a yi yunwa Allah bai sa ba aka zo aka ji kusan kowa ya wadatu to me muke nema ai babu. Alhamdulillahi.
Kina maganar an ba da tallafi ga al’umma, wasu na ganin na kusa ne kawai ake raba wa, me ya sa?
To amma wallahi mu a ce mu muke ci ba gaskiya ba ne domin Injiniya Abba Kabir Yusuf shi ta al’ummarsa yake (mutanen gari) ba ta tamu yake ba, mu da muke kusa da shi din shi yana kyautatawa mutanen gari ku ma kun san da hakan. Mutum zai je da bukata za a rubuta a ba shi sai dai in maciya amana ne suka danne. Tun da yana da maciya amana amma wallahi Injiniya Abba Kabir Yusuf duk sakon da aka kai masa yana ba da wannan sakon ko kwanaki a gaba aka kawo takardar wani bawan Allah za a kai shi asibiti miliyan nawa ne ma? Na manta, amma a gabana aka yi aka bayar, kuma an ba da kudin an fitar da su, duk wani abin karya ne da kuma ‘yan adawa da suke yarfe irin na siyasa amma shi yana taimakawa mutane fiye da tunanin da mutum. Yanzu ni ba zuwa kika yi kika tarar da mai kemis ya kawo min magani ba, kuma a gabanki ya ba ni takardar lissafin wadanda suka karbi magani ba? To ni ce na ba da umarni cewar duk wanda ba shi da shi kuma an rubuta masa magani ko ba shi da lafiya ya je ya karba.
Ni kuma in wata ya yi abin da ya kama ya zo ya karba, ‘yan unguwa da ma wadanda suke tsallake duk suna zuwa su karba, to kin ga wannan wani nauyi ne na dauke wa gwamna na mazabata tun da nace ko ina in ana bukata a zo a fada min to balle shi da yake gwamna mai adalci gwamna dan waliyin Allah mai albarka. Mahaifiyarsa kullum tana yi masa addu’a ai zai gama da duniya lafiya da yardar Allah.
Wane kira za ki yi ga wasu mata ‘yan siyasa da suke yin wasu abubuwa marasa kyau ki ga mace na shaye-shaye ko jagaliyanci wai ita siyasa take yi, wata ma za ta bar gida kwana daya, biyu har mako daya ta tafi harkar siyasa?
To mu kamfen dinmu ba haka yake ba kuma mu siyasarmu ba haka take ba kuma Babanmu Rabi’u Musa Kwankwaso bai dora mu a wannan tafarkin ba, duk wata ‘yar siyasa da za ta bar gida kwana biyu to karya take yi kawai zuwa take yi ta dawo, ba a kwana wurin kamfen ko ni da nake shugaba da zan ce ma in wani abu ya tashi ya kamata in kwana wallahi ban taba kwana ba, in zan kai karfe daya zuwa biyu gidana zan dawo cikin iyalina nake zuwa in kwana da safe in tashi in fita, wadancan su suke lalata kansu suke bata kansu kuma ina kira gare su masu wandannan dabi’ar da su yi wa kansu fada su daina, su sani cewar duk abin da suke yi watarana za a tambaye su a kansa.
sannan ina kara yin tuni a gare su cewar rayuwar ‘ya mace gajeriya ce da zarar kin kai wani minzalin to kina bukatar ki yi aure kina fara haihuwa kuma shikenan rauninki ya baiyana, ko ma me za ki yi za ki yi shi ne kina duba yaranki musamman ma a ce kin fara da ‘ya mace shikenan. Da wannan nake cewa ya kamata su daina yi wa iyayensu karya kuma muma su daina yi mana domin mu suna zaluntarmu suna bata mana jam’iyya domin mu jam’iyyarmu ta adalci ce ta biyayya ce, ban taba ganin yarinyar da za a ce yau an fito kamfen ta kwana ba sai dai in ita ta sa kanta maganar gaskiya mu ba ma haka, domin ba zan taba mantawa ba lokacin ina Shugabar mata Baba Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso zai fito da kansa ya ce; “Women Leader je ki ki debe matan nan naki kowace ta tafi gida. Billahillazi ana sallah karfe takwas ta yi zan je na ce kowace ta tashi ta tafi gida haka zan sallame su kowace in ba ta kudin mota ta tafi gida.
Yanzu ga shi kina rike da ofishi, daga lokacin da kika samu wannan mukaamin zuwa yanzu me kika yi wa mata?
Kin san mu mata muna kaunar mu ga yau a ce ‘yar’uwarmu mace ce ke rike da wani mukami muna ji a jikinmu cewar tamkar mu ne a kan kujerar kuma in batun taimako ya taso mata mu ne a sahun gaba. To kujerar ban dade da samun ta ba kuma kin san harkokin komai sai kana bin sa a hankali musamman harkar siyasa kuma duk abin da za ka yi sai ka yi taka- tsantsan domin gudun kada ka samu matsala.
Bari ki ji wani abin dariya da na yi; albashina na farko duk mata na dinga bi ina rabawa, da fari ‘yan gidana na tara masu yi min wahala mai dubu goma mai dubu biyar haka duk na rarraba albashina naira daya ban ci ba hana rantsuwa na dauki naira dubu sai mahaifiyata da na san na daukarwa dubu biyar haka duk na rabarwa jama’ar Annabi, amma ina nan a karkashin ofis dina zan zauna da Maigirma Gwamna in ga me ya dace in yi wa matan da suka sha gwagwarmaya, ba ma matan ba har da maza don na fada miki ni ta kowa ce. Kin ji babban burina in samu in taimaki mata da maza daga ko ina cikin jihar Kano, ni na san akwai ‘ya’yan Mama da yawa Mama sama Mama kasa ga ‘yan Social media dina wadanda suka taimaka min a tafiya maza da mata, to kin ga ba zan ce ni ta mata ba ce kawai har da maza, ofis dina na kowa ne albarkar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama ina nan kuma zan zauna da Gwmnana mai adalci.
Kin ga saboda irin adalci na Gwamna mutanen da ya diba suka tafi aikin Hajji cikin kaso goma (kaso) tara ba su taba zuwa ba. Ba irin gwamnatin baya ba wadda daga su debi ‘ya ‘yansu sai matansu sai na kusa da su sosai, amma kin ga mu babu wani jami’in da ya tafi, duk muna gida kowa yana nan, duk na kasa aka diba suka tafi, maza da mata, ai kin gani ko a nan gwamna ya kamanta adalci.
To wasu na cewa kujerar ma ta gwamna Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ne ke juya ta, me za ki ce kan haka?
Hhm! Allah Sarki! Shi Babana yana can yana ji da hidimarsa ina ruwansa da mulkin jihar Kano, karya ce kawai da yarfen siyasa. Injiniya Abba Kabir Yusuf shi ne Gwamnan jihar Kano kuma shi yake jan ragamar mulkinsa, adalin Gwamna, muna ta ganin adalci mutanen gari ma suna gani suna fada, mun gode Allah tun da idan kana cikin gwamnati kuma Gwamna yana adalci ribarka ce, jin dadinka ne tun da duk inda ka shiga za a ce Gwamnanka adali ne ka yi sambarka kin ga ba abin da ya fi wannan dadi. Shi Abba ma duk bai san wannan ba. Muna godiya ga jama’ar jihar Kano muna kara godiya ga Allah Subhanahu wata’ala.
Wane irin aiki ofishinki yake yi?
Ofis dina ai yana karkashin majalisar jihar Kano, kamar kin ga akwai daukar ma’aikata maza da mata akwai ba da tallafi da kuma jari shi ma dai ga maza da mata, ina mai addu’ar Allah ya karawa Gwamna lafiya ya karawa Sarki Sunusi lafiya ya kara kare su a duk inda suke aiki, duk mai nufin su da sharri ya mai da masu kansu.
Wanne irin abinci kika fi so?
Eh to gaskiya ina son tuwo, don zan iya cin tuwo da safe tuwo da rana tuwo da daddare, gaskiya ina son tuwo fiye da kowane irin abinci dangin taliya da shinkafa sai kuma jan nama da kaza amma jan nama na rago, ina son kifi amma son da nake yi masa bai kai na naman rago da kaza ba, ina kuma son nau’in kayan marmari kamar musamman Tufa da Inabi.
A kaya wacce kala kika fi so?
Ina son kaya kalar ja kowanne abu ne ina son nau’in ja, don ko kaya na sa mutane na cewa ja yana yi mini kyau sosai, sai kuma launin orange da green.
Mene ne yake burge ki da mutane?
Abin da ke burge ni da mutane shi ne; wadanda ba su da sa ido, ina son mutanen da suka kasance babu ruwansu musamman akan abin da bai shafe su ba, kin ga ai ko addininmu ma ya hore mu da mu bar abin da babu ruwanmu. Shi ya sa wani lokacin rayuwar mutanen dake can gefe take burge ni.
Mene ne kuma ba ki so ga mutane ko ba ki so a yi miki?
Raini! Gaskiya ba na son raini ina son a mutunta ni ni ma na mutunta mutum, amma kin ga raini, ba na son sa ni ma ba zan raina na sama da ni ba kuma ko wane ne ya ce zai raina ni yanzun nan za a ji kanmu da shi. Don haka ina kaunar mutum mai mutunci wanda yake mutunta mutane sannan bana son mai cin amana.
Wane fata za ki yi ga Leadership Hausa?
Ina yi mata fatan dukkan alherin Allah ya kai mata ya ba su ikon rubuta labarai na gaskiya wanda ya fito daga tushe. Allah ya kara daukaka ta, ya sa al’umma su amfana da ita ya sa ta zamo tana sahun gaba, allahumma amin.