Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bukaci shugabannin jam’iyyar PDP a dukkan matakai da su bai wa matasan kasar nan dama domin lashe zaben 2027.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da kwamitin amintattu na kungiyar shugabannin matasan jam’iyyar PDP na shiyya a Abuja, Malam Shekarau ya ce yin hakan zai taimaka wa jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko.
- An Roki Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Tallafi Ga Aikin Hajjin 2025
- Sojoji Sun Kama Mutane 20 Kan Zargin Kashe-kashe A Jihar Filato
Ya kuma umurci matasa da su yi gangamin jam’iyyar PDP a matsayin hanya daya tilo da za ta fitar da Nijeriya daga kalubalen da take fuskanta.
Tsohon gwamnan Kano ya ce jam’iyyar PDP a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki ta samar da dimokuradiyya mai kyau ga al’umma tare da kyautata rayuwa, kuma ya kamata ta dawo kan karagar mulki a 2027.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar matasan jam’iyyar PDP shiyyar arewa ta tsakiya, Aruwa Ismailab ya bayyana cewa kafafen sada zumunta na zamani za su kasance hanyoyin wayar da kan jama’a domin dawo da kwarin gwiwar ‘yan Nijeriya.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da, Shugaban PDP na Jihar Kogi, Hon. Enemona Anyebe da sakataren tsare-tsare na shiyyar arewa ta tsakiya, Dakta Joel E.B Adagadzu da babban jami’in PDP na kasa, Dakta Yunana Iliya da dai sauransu.