Tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya fara jagorantar wata tafiya domin samar da shugabanci na gari a Nijeriya.
Wata tawaga da ya jagoranta zuwa Abeokuta ta ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon ministan tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma, domin neman shawarwari kan manufarsu.
- Yadda Dortmund Ta Barar Da Garinta A Santiago
- Cike Giɓin Ababen More Rayuwa: Nijeriya Na Buƙatar Dala Tiriliyan 3 A Cikin Shekara 30 – Kakakin Majalisa
A yayin ziyarar, tsohon gwamnan na Kano, ya shaida wa manema labarai cewa babban dalilin da ya sa suka fara tuntubar masu ruwa da tsaki shi ne, nemo wa kasar mafita.
Shekarau, ya ce a cikin tafiyar da suka fara suna son su zaburar da al’umma tun daga matakin mazaba har zuwa matakin kasa domin su gano wadanda za su yi musu adalci idan suka ba su shugabanci a Nijeriya.
“Ba mu ce mun fi kowa iyawa ba, amma mun yarda cewa a Arewa da kuma kasar nan baki daya muna da nagartatttun mutane wadanda idan aka ba su dama, za mu zaburar da al’umma domin su hango duk wanda suka san yana da wata gogewa da adalci da kuma gaskiyar da zai jagoranci mutane da adalci, domin mu yi yunkuri mu tallata su, mu fito da su a ba su dama su zo su gabatar da abin da suke yi.
“A yadda ake tafiya an mayar da siyasa ta zama ta kudi, ta zama ta ubangida, suna dora mutane shugabanci ko sun iya, ko ba su iya ba, ko sun dace, ko ba su dace ba, ko suna da kwarewa ko ba su da ita, kuma duk yadda suka dama haka ake sha,” in ji shi.
Shekarau, ya ce suna son su zaburar da ‘yan kasa daga Arewa da ke da kuri’a mafi yawa da ma kasa baki daya su daina la’akari da abin da ake ba su ranar zabe ta yadda wasu ke dasa shugabannin da ba su dace ba.
Kazalika, ya ce za su nemi hadin kan duk wanda yake son bayar da gudunmawa kuma za su samu nasara.
Ya ce babbar manufarsu ita ce a samar da shugabanci na gari a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp