Tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, ya bai wa kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP wa’adin sa’o’i 48 da ya janye dakatarwar da aka yi masa ko kuma ya fice daga jam’iyyar.
Shema ya kuma bukaci da a rusa abin da ya kira “kwamitin riko na jam’iyyar PDP a Jihar Katsina wanda ya ce ba bisa ka’ida ba tare da amincewa da kwamitin zartaswa yake aiki a jihar ba.
- Kamata Ya Yi A Yi Hadin Kai Don Magance Kwayar Cutar COVID-19
- CBN Ya Saki Kudi, Ya Umarci Bankunan Kasuwanci Su Yi Aiki A Ranakun Mako
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 24 ga watan Maris, 2023 kuma zuwa ga shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, Shema ya ce rashin soke yanke shawara kan batutuwa biyu da ya gabatar, ya kamata wasikar ta zama a matsayin ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance daga Asabar, Maris 25, 2023.
“Don haka ba zan iya ci gaba da zama a jam’iyyar PDP a karkashin dokokin Dokta Iyorchia Ayu ba.
“A halin da ake ciki na ci gaba da yin kiraye-kirayen kamar haka: A soke hukuncin da kwamitin gudanarwa na kasa ya yanke na rusa kwamitin zartaswa na Jihar Katsina ba bisa ka’ida ba tare da ba su damar kammala wa’adinsu tare da rusa kwamitin da ake zargin na rikon kwarya.
“A soke hukuncin da kwamitin aiki na kasa ya yanke na dakatar da ni a matsayina na dan jam’iyyarmu cikin sa’o’i 48 masu zuwa.
“Ku lura cewa rashin aiwatar da wadannan canje-canje guda biyu cikin awanni 48, wannan wasikar ta kasance a matsayin ficewata daga jam’iyyar PDP a hukumance daga ranar Asabar 25 ga Maris, 2023.
Idan za a tuna cewa PDP ta mika gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ga kwamitin ladabtarwa tare da dakatar da Fayose, Shema, da Anyim da dai sauransu.