Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da Shirin Inganta Ilimin Sakandare (ASSEP) wanda hukumar raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ke aiwatarwa domin shawo kan matsalolin da suke shafar harkar ilimi a matakin sakandare, musamman magance cire yara daga makarantar sakandare a shiyyar Arewa maso gabas.
Manufar shirin ASSEP ita ce inganta ilimi da koyar da sana’o’i ga ɗaliban da suka kammala karatun sakandare a faɗin jihohin Arewa Maso Gabas guda shida.
- Hajjin Bana: Shettima Zai Kaddamar Da Jirgin Farko Na Maniyyata 430 A Kebbi
- Yadda Ƙungiyar Matasan Arewa Kan Harkokin Tsaro Ta Shirya Tattaunawa Kan Batun ‘Yansandan Jihohi
Da ya ke ƙaddamar da shirin a gidan gwamnatin jihar Bauchi ranar Asabar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada muhimmiyar rawar da ilimin sakandare yake da ita bayan karatun firamare, yana mai bayyana ƙalubalen yankin na Arewa maso Gabas wajen aiwatar da tsarin ilimin bai ɗaya da kuma shawo kan ƙalubalen da al’adu ke yi ga ilimin boko.
Ya ce; yankin Arewa Maso Gabas yana fama da ƙarancin shigar yara makarantun sakandare, wanda bai wuce kaso 19% ba, idan aka kwatanta da alƙaluman shigar yara makarantun sakandare a ƙasa baki ɗaya wanda ya kai kaso 39%. Shettima ya yabawa gwamnonin shiyyar bisa haɗin kai da jajircewarsu wajen inganta yankin.
Manajan Daraktan hukumar ta NEDC, Mohammed G. Alkali ya yi ƙarin haske kan manufofin shirin na ASSEP, waɗanda suka haɗa da; inganta makarantun gaba da sakandire, da bunƙasa sana’o’in hannu, da kuma inganta ƙwarewar malamai.
Alƙali ya jaddada aniyar shirin na mayar da hankali kan shirye-shiryen Kimiyya da Fasaha da Injiniyanci, da Lissafi wato (STEM) da kuma sadarwa, waɗanda ke da muhimmanci wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, da tunani mai zurfi a tsakanin matasa.