Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar tsohon ministan noma da ci gaban karkara, Audu Ogbeh, yana mai cewa Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin shugabanninta masu hangen nesa. Shettima ya bayyana mutuwar Ogbeh a matsayin babban rashi ga shirin sauya fasalin noma da ci gaban ƙasa.
A ranar Litinin, Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zuwa gidan marigayin domin yi wa iyalinsa ta’aziyya. Ya ce gudummawar Ogbeh wajen tabbatar da tsaron abinci da ci gaban karkara za ta ci gaba da kasancewa a tarihin ci gaban Nijeriya. Marigayin ya rasu ranar Asabar yana da shekaru 78, inda mataimakin shugaban ƙasa ya yaba da jajircewarsa wajen inganta rayuwar manoma a faɗin ƙasar.
- Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu
- Nazari Kan Gazawar Tsofaffin Ministocin Noma 52 Da Suka Shude A Nijeriya
Shettima ya bayyana Ogbeh a matsayin jagora mai kishin ƙasa wanda aikinsa ya wuce bambancin siyasa ko yankuna, yana mai cewa tsarin da ya samar wajen haɓaka noma ya zama tsari na ɗorewar ci gaban aikin gona. Ya ce marigayin ya kasance mutum mai gaskiya, da jajircewa, da kishin walwalar manoma da al’ummar karkara.
Mataimakin shugaban ƙasa ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma saka shi da Aljannah Firdaus. Ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalansa, da gwamnati da al’ummar Jihar Benue, da ma Nijeriya baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi, yana mai cewa gadon da marigayin ya bari zai ci gaba da zaburar da masu ruwa da tsaki a harkar noma a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp